Dole A Hukumta Obasanjo Kan Dala Biiyan 16 Na Wutar Lantarki – Oshomole

  0
  782

   Isah Ahmed Daga Jos

  SHUGABAN jam’iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshomole ya bayyana cewa dole shugaban kasa Muhammad Buhari ya gurfanar da tsohon shugaban kasa Cif Olosegun Obasanjo, kan kudin al’ummar Najeriya Dala biliyan 16, da ya fatar kan gyaran wutar lantarki a Najeriya. Shugaban jam’iyyar ta APC ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen   kaddamar da yakin neman zaben gwamnan Jihar Filato Simon Lalong, karo na biyu a garin Jos.

  Ya ce lokacin da tsohon shugaban kasa Obasanjo da mataimakinsa Atiku Abubakar suka yi shugabancin Najeriya, karkashin jam’iyyar PDP sun fitar da kudin Najeriya Dala biliyan 16, kan gyaran wutar lantarki a Najeriya.

  Ya ce a lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya yi tambaya kan ina wutar lantarki take a Najeriya, duk da irin wadannan makudan kudade da aka kashe a lokacin mulkin PDP. Maimakon wadannan mutane su fito su bayar da amsa, sai suka buge  da zargin gwamnatin Buhari kan cewa tana nuna banbanci kan yaki da cin hanci da rashawa da take yi a Najeriya.

  Ya ce don haka dole ne shugaba Buhari ya sanya  Obasanjo ya fito ya yi bayani kan yadda ya kashe wadannan kudade.

  Oshemole ya yi bayanin cewa bai kamata ‘yan Najeriya su zabi Atiku Abubakar a matsayin shugaban Najeriya ba, domin idan suka zabe shi zai sayar da Najeriya.

  ‘’Abin da yasa jam’iyyar PDP da Obasanjo suke zargin shugaba Buhari da hukumar EFCC kan cewa suna zabe kan yaki da cin hanci da rashawa da ake yi, saboda basu bincike su bane.’’

  Ya yi kira ga al’ummmar Jihar Filato su sake zaben gwamna  Lalong da shugaban kasa Buhari a zaben da za gudanar.

  A nasa jawabin gwamna Lalong ya bayyana cewa shi a wurinsa bai dauka cewa shugaba Buhari yana takara da wani a Najeriya ba. Domin babu wanda al’ummar Najeriya zasu zaba sai Buhari.

  ‘’Shugaba Buhari mai gidana ne domin a duk lokacin da na bukaci ya taimake ni, kan wani abu nan take yake taimakona. Buhari ya kawo mana zaman lafiya, ya yi mana abubuwa da dama a Jihar nan’’.

  Ya ce babu  jam’iyyar PDP  a Jihar Filato  domin ta riga ta mutu.

  A wajen wannan taro wanda ya sami halartar dubban magoya bayan jam’iyyar APC, daga dukkan Kananan Hukumomin Jihar. Shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshomole ya karbi wasu manyan ‘yan siyasar Jihar, da suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC.

  Wadannan manyan ‘yan siyasa sun hada da tsohon dan takarar gwamnan Jihar karkashin jam’iyyar AFGA Ambasada Chiris  Giwa da Alhaji Abubakar Dashe da Loranzo Gwatu da Cif Simon Ngwan da dai sauransu.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here