Hukumar EFCC Tayi Karin Haske Game Da Labarin Maganar Tsige Magu

0
662

Daga Usman Nasidi 

HUKUMAR nan ta gwamnatin tarayya dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC tayi karin haske game da labarin maganar cire Mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu da ake ta yadawa a kafafen sadarwar zamani.

Hukumar a ta bakin jami\’in hulda da jama\’ar ta, Mista Tony Orilade da yake bayar da karin haske game da lamarin yayin zantawar sa da manema labarai yace maganar ba tada tushe ma balle makama don kuwa kanzon kurege ce.

Mista Tony Orilade ya kara da cewa a yanzu shi Mista Magu ba abunda ke gaban sa ma sai karin jajircewa da yayi domin ganin ya kakkabe kasar daga dukkan cin hanci da rashawa.

A baya dai mai karatu zai iya tuna cewa an yi ta yamadidi da labarin cewa Mista Ibrahim Magu za\’a tura shi karatu domin ya sauka daga kan mukamin sa a dora wani.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here