Kada Gwamnati Ta Hana Shigo Da Taki Daga Waje-Sarkin Noman Bassa

0
649

Isah Ahmed Daga Jos

GARKUWAR al’ummar Hausa Fulani na yankin Pengana kuma Sarkin noman Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi kira ga gwamnatin tarayya  kada ta hana shigo da takin zamani daga Kasashen waje zuwa Najeriya. Alhaji Ya’u Bala Jingir ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

Ya ce wannan kira ya zama wajibi, jin irin rade radin da ake yi cewa kamfanonin yin takin zamani na Najeriya suna ta kokarin ganin gwamnati ta hana shigo da taki daga kasashen waje.

Ya ce hana shigo da taki zuwa Najeriya daga waje wata  babbar matsala ce ga manoman Najeriya. Domin kamfanonin takin da muke da su a Najeriya, ba zasu iya wadatar da manoman Najeriya da taki ba. Kuma  basa yin taki ingantatce, suna hada abubuwan da suka ga dama ne kawai a takin da suke yi. Don haka bai kamata gwamnati ta hana shigo da taki daga waje ba.

 ‘’Takin da ake shigowa da shi daga  waje ne kawai yake da inganci. Kamfanonin taki na Najeriya ne suke son a hana shigo da taki daga waje. Bayan takin da suke yi bashi da kyau, babu shakka idan aka dogara da takin da ake yi a Najeriya, noma ba zai inganta ba’’.

Daga nan ya yi kira ga  gwamnati ta  samar da taraktocin noma da  takin zamani ga manoma. Kuma ta sayi kayayyakin noma da  daga hanun manoma ta ajiye,   yin haka zai dada bunkasa harkokin noma a Najeriya. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here