Kungiyar Cigaban Makarfi Tashirya Taron Jin Kudurorin ‘Yantakarkaru Na Majilasun Jiha Dana Tarayya

0
660

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

KUNGIYAR ciyar da karamar hukumar makarfi a karkashin jagorancin shugabancin ta Ibrahim Aliyu Alhassan, ta shirya taron jin kudurorin ‘yan takarkarun majilasun dokokin jihar kaduna da majilasar kasa da suka fito daga jam’iyun siyasu daban daban idan Allah ya kai su ga lashe kujerun da suke nema.

Kungiyar ta shirya taron ne a dakin taro na kwalejin koyar da aikin kiwon Lafiya   dake karamar hukumar makarfi.

Kungiyar ta shiyar taron ne sabo da ganin cewa lokaci yayi da sai al’umar karamar hukumar makarfi sun san dalilin tsayawar takarar dan takara da kuma irin cigaban da zasu kawo wa karamar hukumar.

A inda ‘yan takarar majilasun na tarayya da na majilasun jiha su kai ta fadar albarkacin bakin su tare da yin alkawura daban daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here