Wani Malamin Addinin Musulunci Ya Gina Gidan Marayu A Garin Jos

0
1215

Isah Ahmed Daga Jos

WANI fitattacen Malamin addinin musulunci da ke zaune a garin Jos babban birnin Jihar Filato kuma Daraktan Gidaunar Anwarul Faidah Sheikh Harisu Salihu ya gina wani babban gidan marayu a garin Jos.

Da yake jawabi a wajen taron bude  gidan  Kwamishinan Sufuri na Jihar Filato Malam Muhammad Ahmed  Nazifi ya bayyana cewa  wannan aikin gina gidan marayu  yana daya  daga cikin ayyukan  sadakatu jariya.

Ya ce gidan marayun   shi ne na farko da wani mutum daya ya gina kuma shi ne na farko  a cikin al’ummar musulmin Jihar Filato. Domin dukkan gidajen marayun da ake da su a Jihar, kungiyoyi ne suka gina.

Ya yi kira ga sauran al’umma su yi koyi da wannan mutum wajen gina irin wadannan gidaje, domin tallafawa marayu.

A nasa jawabin Sakataren gudanarwa na  Kungiyar Jama’atu Nasril Islam reshen Jihar Filato Sheikh Abdul’azeez Yusuf ya yi kira   ga Kungiyoyin addinin musulunci da sauran Kungiyoyi masu zaman kansu su baiwa wannan gidan marayu goyan baya da hadin kai 

Ya ce babu shakka  wannan gidan marayu  wuri ne da ya kamata a taimaka masa.

Shima a nasa jawabin wani babban darakta a ma’aikatar  mata ta Jihar Filato Mista Joseph Gwaisan ya yi bayanin cewa sun baiwa wannan gidan marayu izinin gina gidan batare da bata lokaci ba. Domin an cika dukkan ka’idojin da suka kamata.

Ya yi  kira ga jama’a da suke son bude irin wannan gida su bi ka’idojin gwamnati wajen bude su.

Tun da farko a nasa jawabin wanda ya gina gidan marayun Sheikh Harisu  Salihu ya bayyana cewa babban abin da ya karfafa masa gwiwar gina wannan gida, shi ne ganin irin mawuyacin halin da marayu suke ciki ne. Don haka ya gina  gidan domin ya tallafawa marayun.

Ya ce wannan aiki da ya yi bai dauka ya yi wani abu ba. Kuma tun da ya fara aikin   babu wani dan siyasa da ya taimaka masa.

Ya ce wannan gida zai dauki marayu guda 40 ne, maza  20 da mata  20.

Ya ce suna da ma’aikata 14  da zasu rika aiki a gidan ana biyansu albashi a duk wata. 

‘’Wadannan marayu guda 40, mun dauki ‘yan shekara 5 ne  zamu rike su har su kai shekara 13 kafin mu yaye su. Za a rika yi masu abinci a kullum.  Kuma zamu sanya su a makarantarmu muna son kafin mu yaye su, su haddace Alkura’ani mai girma’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here