Atiku Ya Yi Alkawarin Magance Rikice Rikicen Jihar Filato  

  0
  761

  Isah Ahmed Daga Jos

  TSOHON mataimakin shugaban kasa kuma Dan takarar kujerar shugabancin kasar nan, karqashin jam’iyyar PDP Wazirin Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin  idan aka zabe shugaban kasa, a zaben da za a gudanar a ranar 16 ga wata mai zuwa, zai magance rikice rikicen da ake fama da su a Jihar Filato. Alhaji Atiku Abubakar ya yi wannan al’kawarin ne, a lokacin da yake jawabi a  filin wasan polo na garin Jos, lokacin da tawagar yakin neman zabensa ta isa garin Jos, a karshen makon da ya gabata.

  Ya ce na farko na  daukar maku alkawarin   zan dawo da zaman lafiya a Jihar Filato. Kuma  na yi alkawari zan samarwa matasa ayyukan yi.

  Ya ce jam’iyyar APC  ta gama a Najeriya, don haka  basa iya magana da al’ummar Najeriya, domin sun san al’ummar Najeriya ba za su zabe su ba. Don haka suke son su yi murdiya a  zababbukan da za ayi.  

  Atiku Abubakar ya yi bayanin cewa APC  babu abin da ta kawo a Najeriya, sai yunwa da talauci da rashin zaman lafiya.

  A nasa jawabin Daraktan yakin neman zabe na Atiku Abubakar kuma shugaban majalisar dattawa Sanata Abubakar Bakola Saraki ya bayyana cewa  lokacin da jam’iyyar APC ta karvi mulkin kasar nan, ta yi alkawarin samar da tsaro da samarwa matasa ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin kasar nan,  amma duk ta gaza cika wadannan alkawura da ta dauka.

  Ya ce yau a Najeriya babu tsaro babu abinci sai yunwa .

  Ya ce babu shakka idan jama’ar Najeriya suka zabi Atiku Abubakar zai magance wadannan matsaloli.

  Shima a nasa jawabin tsohon gwamnan Jihar ta Filato kuma Sanata mai wakiltar mazabar Filato ta arewa, Sanata  Jonah Jang ya bayyana cewa irin taruwar  da al’ummar Filato suka yi a wannan wuri, ya nuna cewa PDP ta cinye zabubbukan da za ayi nan bada dadewa ba.

  ‘’Sun ce bamu iya ba, amma an basu sun kasa yi.  Jama’a  sun  ga irin ayyukan da PDP tayi  a Jihar Filato da Najeriya baki daya.  Tun da APC suka karvi mulki babu wani abu da suka yi, sai kawo yunwa da talauci. Don haka a dawo da Atiku Abubakar a zabe zuwa mai, domin shi  ne zai magance yunwar da wannan gwamnati ta kawo a Najeriya’’.

  A nasa jawabin tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ibrahim Mantu cewa ya yi Jihar Filato gidan PDP ne, domin a nan ne aka haife ta kuma ana ne aka zabi shugaban kasa Obasanjo  da Atiku a matsayin mataimakinsa karkashin PDP.

  Don haka ya yi kira ga  al’ummar Filato su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Atiku a zabe mai zuwa.

  Shi dai wannan taron gangamin yakin neman zave ya sami halartar dan takarar kujerar gwamnan Jihar karkashin PDP Janar Jerimiar Usaini,  da ‘yan takarar kujerun Sanatoci da ‘yan takarar majalisun wakilai na tarayya da ‘yan takarar majalisar Jihar karkashin jam’iyyar,  da sauran magoya bayan jam’iyyar daga dukkan Kananan Hukumomin Jihar.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here