Bai Kamata  Miyetti Allah Da Kautal Hore  Su Nuna Gayon Baya  Ga Buhari Ba-Sale Bayari

  0
  1320

   Isah  Ahmed Daga Jos

  ALHAJI Sale Bayari shi ne  Shugaban Kungiyar cigaban al’ummar Fulani ta Nijeriya ta Gan Allah. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana cewa goyan bayan da Kungiyoyin Fulani na Miyetti Allah da Kautal Hore  suka yi ga takarar shugaban kasa, Muhammad Buhari ba kamata ba. Domin  yin hakan  ba zai taimaki shugaba Buhari ba,  kuma ba zai taimaki al’ummar fulanin Najeriya ba.

  Ga yadda tattaunawar ta kasance

  GTK: Mene ne matsayin kungiyarku  kan  takarar  shugaba Buhari da Atiku Abubakar, ganin cewa dukkansu Fulani ne?

  Sale Bayari: Wato  wannan  Kungiya ta Gan Allah kungiya  ce ta cigaban al’ummar fulanin Najeriya. Kuma kamar yadda na taba fada, kungiyar ba kungiyar Fulani makiyaya ba ce kadai. Kungiya ce ta dukkan wani bafulatani kowace irin sana’a yake yi, yana da yancin ya je yayi a matsayinsa na dan kasa.  

  Don haka bai kamata mu ce ga ‘dan takarar da muke goyan ba. Domin bamu da wata  akida ko  manufa kan aika  wannan al’amari.

  Saboda akwai hadari  cikin irin wannan al’amari, musamman ganin cewa wadannan ‘yan takara guda biyu shugaba Buhari da Atiku Abubakar dukkansu Fulani ne. Don haka dukkansu namu ne. Saboda  haka ba zamu ce, ga namu ba. Wanda duk ‘yan Najeriya suke so shi ne namu. ‘ Idan muka ce ga wanda muke so tsakanin wadannan ‘yan takara wadansu  ‘yan wannan kungiya zasu iya darewa,  su ce bamu yi masu adalci ba. Saboda haka kungiyarmu ba zata iya fitowa fili, ta ce ga dan takarar da take goyan baya ba.

  Abin da ya kamata mu yi shi ne mu  duba  wadannan ‘yan takara kan  mene ne suka yiwa al’ummar Fulani a baya, kuma idan muka zabe su mene ne zasu yiwa al’ummarmu.  

  Misali kamar tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar lokacin da yake mataimakin shugaban kasa, mene ne ya yiwa al’ummar Fulani?. Ko kuma mene ne zai yiwa al’ummar Fulani idan suka zave shi?

  Haka shima shugaba Buhari ya yi shekaru 4 yana mulkin kasar nan. A cikin wadannan shekaru mene ne ya yiwa al’ummar Fulani?. Ko kuma wadanne alkawura ya yiwa al’ummar Fulani kuma ya cika?. Musanmman ganin irin damuwar da al’ummar Fulani makiyaya suke ciki a Najeriya.

  Domin  kwanakin baya mun ji labarin cewa gwamnatin  shugaba Buhari ta fito da kudi naira biliyan 60, ta baiwa manoman da suka yi asara, sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi.

  A cikin shekarun nan mu al’ummar Fulani mun yi asarar mutane sama da dubu 3 tare da sace mana dabbobi  a rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma. Amma zuwa yanzu ba a yi mana taimakon  komai ba.  Saboda haka mu Qungiyar Gan Allah wanda ya fito ya ce ga abin da zai yiwa al’ummar Fulani shi ne namu.

  GTK: Kwanakin baya kungiyoyin Fulani makiyaya na Miyetti Allah da Kautol Hore sun fito sun nuna goyan bayan su ga takarar shugaban kasa Buhari, mene ne zaka ce kan wannan matsaya da wadannan kungiyoyi suka dauka?

  Sale Bayari: Babu shakka mun ga Kungiyar Miyetti Allah ta kira Fulani  zuwa Abuja suka yi taro suka fito suka ce  sun dauki shugaba Buhari a matsayin wanda zasu zaba.

  Bayan mako guda sai Kungiyar  Kautal Hore ta kira taro a Abuja, itama ta ce tana goyan bayan shugaba Buhari. Kuma tana tsinewa Atiku  saboda  wai ya yi wasu maganganu wadanda basu yi masu dadi ba. Kuma suka ce ya hada baki da kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International,  inda ta ce an kashe mutane sama da dubu 3, amma basu yarda da sahihancin wannan rahoto ba. Amma wai Atiku yana da hanu  cikin wannan magana, don ya ce idan Buhari ya cigaba da mulki ba a za sami zaman lafiya ba, tsakanin makiyaya da manoma.

  Maimakon kungiyar Kautal Hore su tsaya kan abin da suka sanya a gaba, su fito su ce suna tare da shugaba Buhari. Sai suka fito suka rabe da wannan magana da Atiku ya yi, wanda ba manufarsa ke nan ba.

  Abin da kungiyar miyetti Allah ta yi ya nuna kamar suna zuwa su sayar da al’ummar Fulani ne. Saboda biyan buqatarsu, domin ban ga dalilin da zai san ya su gayyato al’ummar Fulani daga wurare daban daban zuwa Abuja ba, su ce wai sun zo su nuna amincewarsu ga takarar shugaba Buhari ba.

  Ina ganin wannan abu da suka yi, basu taimaki shugaba Buhari ba. Saboda tun tuni akwai wasu manoma da suke zargin cewa makiyaya suna kashe su. Suma makiyaya suna cewa wasu manoma suna kashe su, suna kwase masu dabbobi, kuma gwamnati bata dauki wani matakin magance wannan matsala ba.

  Wasu suna cewa ai shugaban kasa Buhari a matsayinsa na bafulatani kuma uban kungiyar miyetti Allah, shi yasa yaki ya yiwa Fulani wani abu kan abubuwan da suke faruwa.

  Har’ila yau  wasu manoma da wasu ‘yan boko da ‘yan tada zaune tsaye suna cewa ai wannan kungiya ta Miyetti Allah wani reshe ne na ‘yan ta’addar fadar shugaban kasa.

  Saboda haka ni ina ganin  akwai rashin basira  su fito,  su  nuna cewa suna tare da shugaba Buhari, batare da bayar da wasu kwararan dalilai ba. Basu fadi abubuwan da aka yiwa al’ummarsu ba, wanda suke ganin ya cancanta su goyi bayansa. Ni ina ganin kamar suna dada tsoratar da wasu mutane ne wadanda ba Fulani ba, cewa akwai wata dangantaka tsakani Buhari da wannan al’umma.

  Kuma kamar Kungiyar Kautal Hore sun yi ta zagin  Atiku Abubakar  a wajen wannan taro da suka yi.

  Sai naga wadannan ‘yan takara  dukkansu Fulani ne kuma  dukkansu suna da hakki karkashin wadannan kungiyoyi na  su yi masu adalci. Maye zai sa ka fito kana zagin mutum kan siyasa? wannan ba daidai bane.

  GTK: Wato  kana ganin  wannan abu da wadannan kungiyoyi suka yi, ba zai taimaki Buhari da al’ummar Fulani ba?

  Sale Bayari: Babu shakka ba zai taimake su ba, saboda naka ba sai kaje kasuwa kana tallan  cewa naka naka ne ba. Kowa ya san naka naka ne.

  Ya kamata a bar Fulani wadanda suke jam’iyyar APC  suje su yi ta yin tarurrukansu suna nuna goyan bayan su, ga Shugaba Buhari. Haka suma fulanin da suke jam’iyyar PDP, abar su suje su nuna goyan bayansu ga Atiku.

  Amma bai kamata a kawo sunan wata kungiya ta Fulani wadda ta kowa da kowa ce a ce ana goyan bayan shugaban kasa ba. Wannan ba a taimaki shugaban kasar ba, kuma ba a taimaki al’ummar Fulani ba.

  Domin an kawo wani abu wanda zai sanya a gobe idan ya yiwa Fulani wani abu ace ya yi ne domin fulani   nasa ne. Ko kuma idan bai yi mana wani abu ba, za a iya yi mana dariya.

  GTK: To karshe wannan sako ko kira ne kake da shi zuwa ga al’ummar Fulani?

  Sale Bayari: Abin da nake son na ja hankali ‘yan uwana al’ummar Fulani na Najeriya shi ne mu yiwa Allah godiya, domin shugaban kasa da yake kan mulki namu ne. Idan Allah ya sake bashi mulkin Najeriya namu ne. Idan Allah bai sake bashi ba namu ne.  Dukkan wadannan ‘yan takara Buhari da Atiku namu ne kuma suna taimaka mana ta hanyoyi da dama.

  Saboda na tuna wani lokaci da Atiku ya kafa wani kamfanin yin abincin shanu, naga ‘yan Miyetti Allah da ya gayyata a wajen bude wannan kamfani. Saboda haka ko yana shugaban kasa ko baya shugaban kasa, bai manta da al’ummarsa ba. Haka shima shugaba Buhari ko yana shugaban kasa ko baya shugaban kasa namu ne. Domin  zamu iya zuwa Daura muje gonarsa mu sha nono, mu ga yadda yake kiwon shanunsa.

  Don  haka ina kira ga al’ummar  fulanin Najeriya mu tsaya mu duba mu ga manufofin wadannan ‘yan takara kan  mene ne zasu yiwa al’ummar Fulani idan muka zabe su?.

  Domin a shekara ta 2015 kungiyoyin Miyetti Allah da Kautal Hore  sun goyi bayan tsohon shugaban kasa Goodlurck Jonathan ne. Kamar kungiyar Kautal Hore har matsayin uban kungiyar   ta bashi

  Kungiyar Miyetti Allah ita kan ta a wancan lokacin ta goyi bayan Goodlurck  ne, domin muna da labari. Tun da sun yi wannan abu a wancan lokacin, yanzu kuma sun zo sun ce suna goyan bayan Buhari ba laifi bane. Amma kuma su so Buhari a yadda ba zasu nuna cewa akwai wani da suke ki ba. Kuma ba sai sun yi zage zage na bata wanda suke ki ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here