Yajin Aikin ASUU: Buhari Ya Bawa Ministan Kwadago Umarnin Gaggawa

0
671

Daga Usman Nasidi

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya bawa ministan kwadago da samar da aiyuka, Sanata Chris Ngige, da ya kawo karshen yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke yi.

Da yake magana a wurin taron cigaba da tattaunawa tsakanin wakilan gwamnatin tarayya da shugabannin kungiyar ASUU, Ngige ya bayyana cewar shugaba Buhari ya matukar damu da cigaba da zaman da daliban jami’o’i ke yi a gida.

Ngige ya kara da cewa shugaba Buhari ya bashi umarnin gaggawa a kan ya kawo karshen yajin aikin domin dalibai su koma makaranta, su cigaba da karatu.

“Shugaba Buhari ya bukaci kar na yi bacci a daren yau har sai na tabbatar da cewar na warware matsalar kungiyar ASUU, sun janye yajin aiki domin dalibai su koma makaranta. Kazalika ya umarce ni na shaida ma ku cewar akwai bukatar kowanne bangare su yi sadaukar wa domin a samu sukunin shawo kan yahin aikin cikin sauki,”a cewar Ngige.

Ministan ya cigaba da cewa, shugaba Buhari ya matukar damu da halin da jami’o’in kasar nan ke ciki tare da bayyana cewar shugaban na da tanadi na musamman domin kawo karshen dukkan kalubalen da bangaren ilimi ke fuskanta a ksar nan.

A yau, Litinin, ne aka cigaba da tattauna wa tsakanin shugabannin ASUU da gwamnatin tarayya a kan yajin aikin da malaman jami’o’in su ka shiga tun watan Nuwamba na shekarar 2018.

An fara tattaunawa ne tun misalin karfe 5:00 na yamma kuma ba a kammala taron ba har zuwa lokacin da aka buga wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here