Zamu Farfado Da Tattalin Arzikin Jihar Kano – Inji Dan Takarar AGA

  0
  720

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano

  DAN takarar gwamnan jihar Kano a tutar jam’iyyar All Grassroots Alliance, (AGA), Alhaji Ahmad Tijjani Sani Darma yace  idan aka zabe shi zai yi kokarin farfado da  tattalin arzikin jihar  ta hanyar inganta masana’antu da  sauran hanyoyi na samar da aiyukan yi ga al’uma.

  Yayi wannan albishir he cikin wata hirar su da wakilin mu a garin Kwa dake  yankin karamar hukumar Dawakin Tofa, inda yace  ko  shakka babu idan aka farfado  da masana’antu tattalin arzikin jihar ta kano zai habaka, sannan za’a Kara samun aiyukan yi musamman a wannan lokaci na dogaro da  kai.

  Alhaji Ahmad Tijjani Darma  ya sanar da cewa idan al’umar jihar kano suka zabi jam’iyyar AGA, babu shakka za’a sami managarcin ci gaba ta kowane fanni, sannan kowane bangare na jihar zai rabauta daga aiyukan raya kasa batare da  nuna bambancin ra’ayin siyasa ba, tareda yi Kira ga malaman addini dasu Kara shiga cikin harkokin siyasa son samun madafar ikon taimakawa kasa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here