Kungiyar PDP Ta Shiga Hadin gwiwa Da APC Don Tazarcen Buhari

0
777

Daga Usman Nasidi

WATA kungiya ta jam’iyyar PDP mai suna Diplomatic Youth Movement of Nigeria (DYMN) ta shiga wata hadin gwuiwa da wata kungiyar ta jam’iyyar APC mai mulki mai suna Youth Mobilisation and Sensitisation (CYMS) domin samun nasarar tazarcen shugaba Buhari.

Shugaban kungiyar ta Diplomatic Youth Movement of Nigeria (DYMN), Malam Yunusa Mohammed shine ya sanar da hakan ranar Laraba a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Hakazalika Malam Yunusa da yake karin haske game da hadin gwuiwar, yace sun ajiye bambancin jam’iyya wuri daya ne domin nemar wa kasa makoma mai kyau da yace Shugaba Buhari ne kadai zai iya tabbatar da hakan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa ‘yan takarkarin shugaban kasa a jam’iyyar APC da PDP yanzu haka suna kan zagaya Najeriya ne suna neman goyon bayan al’umma a zaben da za’a gudanar kasa da wata daya mai zuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here