Udom Emmanuel Ne Zabin Mu – Inji Ibesikpo Asutan

  0
  821

  Mustapha Imrana Abdullahi

  A YAYIN da zaben Gwamna na shekarar 2019 ke kara karatowa, al’ummar karamar hukumar Ibesikpo Asutan sun kara jaddada cewa ba su da zabi Sai Gwamna Udom Emmanuel.

  Mutanen karamar hukumar sun bayyana matsayin nasu ne a ranar Talatar da ta gabata lokacin da Jirgin Yakin Neman Zaben Gwamna Udom Emmanuel ya sauka a karamar hukumar Ibesikpo Asutan.

  A jawabansu daban daban, ta hannun shugabannin su sun tabbatar da cewa mulkin Gwamna Udom Emmanuel ya yi aikin azo a Gani wanda hakan na matsayin wata alamar lallai akwai Karin muhimman al’amura da za su zo nan gaba idan Gwamnan ya sake dawowa a karo na biyu.

  Mutanen karamar hukumar Ibesikpo Asutan sun bayyana cewa hakika sun samu nasarar samun muhimman ayyukan raya kasa tare kuma da bayar da manya manyan mukamin Gwamnati ga yan asalin karamar hukumar.

  A jawabinsa na maraba, shugaban karamar hukumar Ibesikpo Asutan, Mista Sylvester George, cewa ya yi yana da tabbacin cewa Gwamnan zai lashe zabensa a karamar hukumar musamman ganin irin yadda Gwamnan ya yi ayyukan ci gaba a ko’ina don haka dukkan al’ummar suke goyon bayansa kuma sun Bada tabbacin shi ne zabinsu a ranar zabe domin Gwamna Udom Emmanuel ya ci gaba da aiwatar da kyakkyawan jagorancin da yake yi.

  Yana Mai jaddada godiyarsa ga Gwamna bisa irin yadda ya ciyar da karamar hukumar gaba cikin sauri, don haka suke tabbatar Masa da cewa za su mayar da biki ta hanyar yi wa Gwamna Udom Emmanuel ruwan kuri’a domin ya sake darewa.

  Shugabar mata ta Jam’iyyar PDP Misis Ime Orok, a jawabinta tabbatar wa da tawagar Gwamnan ta yi na cewa tuni su mata sun dade suna yi wa Gwamnan Kamfe ga jama’a musamman ta hanyar yada irin Ayyukan da Gwamnan ya yi masu har ma da wadanda ya aiwatar a wadansu wurare a fadin Jihar don haka ta ce suna da tabbacin samun nasarar Gwamnan a zabe Mai zuwa

  Shugabar matan ta kuma yi godiya ga Gwamnan game da farfado da masana’antar sarrafa Rogo a karamar hukumar Ibesikpo Asutan da kuma Gini Mai Hawa Goma sha shida wanda hakan ya kara bunkasa harkokin kasuwanci sosai.

  Ta ci gaba da tabbatar da cewa bisa la’akari da irin yadda Gwamnan ya yi ayyukan raya jihar Akwa Ibom ya zamar wa mata dole su sauke nauyin da yake Kansu a ranar zabe domin Gwamna Udom Emmanuel ya sake dawowa a karo na biyu.

  A jawabinsu na girmamawa Dan majalisar dokokin jihar Mai wakiltar karamar hukumar Ibesikpo Asutan Honarabul Aniekan Uko da kwamishinan Kudi na jihar Mista Linus Nkan, baki daya su cewa suka yi ba su da wani Dan takarar Gwamna tun da Gwamna Udom Emmanuel ya yi aikin azo a Gani har a gaya wa duniya ga irin abin da ya aiwatar domin jihar tare da jama’ar ta da kasa baki daya su ci gaba.

  Sun kuma godewa Gwamnan bisa irin yadda ya cika alkawarinsa na samar da masana’antu da kuma samar da zaman lafiya wanda ya yi maganin irin yadda a can baya jihar ke fama da batun Kashe Kashe da suke da nasaba da siyasa, satar Jama’a da suka hada har da yara domin ba a barsu ba.

  Tun da farko shugaban siyasar yankin Yarima Uwem Ita Etuk, gargadi ya yi ga yan adawa a kan Shirin da suke yi na aikata nauyin zabe.

  Ya Shawarci baki dayan wadanda aka ba aikin yin wannan magudi a yankin da su guji zuwa yankin karamar hukumar Abesikpo Asutan domin jama’ar karamar hukumar a shirye suke su Nuna rashin amincewa ga duk Mai son aikata magudin zabe.

  Yarima Etuk ya ci gaba da cewa ba za su amince a kasa kawo masu kayan zabe cikakku ba da suka yi daidai da yawan masu keda kuri’a hakika ba za su amince da irin wannan daga duk wani malamin zabe ba domin jama’ar yankin za su kalli wanda ke kokarin yin magudi a matsayin makiyi a Gare su.

  Ya kara da cewa idan ma akwai Shirin da ake yi na a kawo kayan zaben da ba su cika ba, to, a wallafa bayanin hakan a manyan jaridun kasa saboda mutanen yankin ba za su amince da duk wani nau’in magudin da zai tauye masu hakkin yin zabe.

  Shugaban siyasar ya kuma yi kira ga jama’a da kada su ji tsoron wadansu daga Gwamnatin tarayya, wanda ya ce wadansu mutane na bugun gaba da hakan. Ya jaddada wa jama’ar cewa karfin al’umma da suke da shi ne abin la’akari a duk wani zabe.

  A jawabinsa Sanata mainwakiltar yankin Arewa maso Gabas a majalisar dattawan dagab jihar Akwa Ibom Sanata Basset Albert cewa ya yi Allah ba zai ba tsohon Gwamnan jihar ba Sanata Godswill Akpabio ya hada Kai da wadansu mutane can da ban domin hana Gwamna Emmanuel dawowa a karo na biyu.

  Ya jaddada cewa ayyukan da Gwamna ya yi tare da irin kyawawan halayensa za su bashi damar sake lashe zabe a karo na biyu.

  Da yake bayar da misalin irin yadda ya kalli gangamin Yakin Neman Zaben APC a ranar Litinin cewa ya yi “na kalli irin yadda masu hadakai suke tabbatar da cewa lallai su yan hadin baki ne kawai.don haka muke gaya masu cewa babu wani batun hadin baki da zai samu nasara”.

  “Mai girma Gwamna Allah yana sonka don haka shi ne zai tabbatar da gaskiya, Allah da ya tsayawa Obong Attah da Akpabio zai tsaya Maka. Allah ba zai bar Akpabio ya samu nasara ba musamman irin yadda yake kokarin hada baki da wasu a kanka.Yadda ya yi shekaru Takwas, kaima Sai ka cika Takwas”.

  Da yake tofa albarkacin bakinsa Darakta Janar na Yakin Neman Zaben Otuekong Idongesit Nkanga, cewa ya yi karamar hukumar Ibesikpo Asutan na yankin mazabar dan majalisar dattawan Uyo ta tsakiya ne lallai mutanen za su tsaya domin kare irin yadda suka bayyana cewa Gwamna Emmanuel Sai ya lashe zabe karo na biyu.

  Ya kuma yi jinjina ga daukacin yayan asalin karamar hukumar Ibesikpo Asutan da suka hada da Eyo Uyo,Obong Victor Attah da babban sojan sama Iya marshal Nsikak Eduok.

  Ya kuma kara da yin kira ga daukacin al’ummar yankin da su zabi Gwamna Udom Emmanuel don ya samu gagarumin rinjaye a tsakanin Gwamnonin PDP a duk fadin Nijeriya.

  A jawabinsa Gwamnan Jihar Akwa Ibom Udom Emmanuel bayyana Jin dadinsa ya yi bisa irin yadda jama’a suka fahimci irin Ayyukan alkairin da ya aiwaatar a duk fadin Jihar baki daya. Ya Yi alkawarin Karin ayyukan alkairin idan ya sake darewa karo na biyu domin jama’a su samu romon dimokuradiyya.

  Dan takarar Gwamnan na PDP ya yi kira ga daukacin jama’a da su tabbatar sun aiwatar da damar da tsarin mulkin kasa ya ba su na zaben mutumin da suke so.

  Ya Yi bayanin cewa mutumin da ya Yaki wanda ya Gada yake kokarin Yakin wanda shi kuma ya gaje shi lallai abin a duba ne samun akwai damuwa kwarai.
  Ya ce dukkan abin da kake bukata a cikin sabuwar Nijeriya zaka same shi a Ibesikpo Asutan. Don haka al’ummar Ibesikpo Asutan Ku yi hankali kada wani ya karkatar da Ku.

  Da akwai wadansu mutanen da suka zo da majami’a saboda haka nazo in yi addu’a tare da aiki ta yadda zaku gane cewa akwai wani da ya yi Gwamna Amma ya Yaki mutumin da ya Gada mutumin da ya bashi kwamishinan shekaru shida, don haka idan mutum zai yi fada da wanda ya karbi Mulki a hannunsa sannan ya yi fada da wanda gaje shi lallai kun san akwai matsala kwarai, domin wannan yana da matsalar

  Gwamna Emmanuel ya ce gaba da bayanin cewa yana tausayawa Dan takarar Gwamnan APC Obong Nsima Ekere kamar yadda ya ce an yaudare shi an karkatar da shi ne kawai, kamar dai yadda aka yaudari Umana Okon Umana a lokacin zaben shekarar 2015 da ya gabata.

  Gwamna Emmanuel ya kuma kara fadakar da masu zabe cewa su tsaya tsaf su goyi bayan mutanen da suke son ci gabansu da koda yaushe suke tare da su har a cikin zuciya domin yin hakan zai kara bayar da damar samun ci gaban jihar tare da mutanen ta da kasa baki daya.

  A wurin taron an ga shugaban Jam’iyyar PDP na jihar Obong Paul Ekpo, ya karbi yayan Jam’iyyar APC da suka canza sheka zuwa PDP.

  Masu canza shekar suna karkashin jagorancin Cif E.O. Etim da kuma Anima Brown wadanda suka ce su ne suka kawo Jam’iyyar APC a yankin don haka a halin yanzu babu ita a yankin sam Sam
  a karamar hukumar Abesikpo Asutan.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here