Buhari Ya Dakatar Da Shugaban Alkalan Najeriya, Walter Onnoghen

0
631

Daga Usman Nasidi

Labarin da ke shigo mana yanzu-yanzu na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi.

Majiyarmu ta samu labarin cewar hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafofin sada zumunta. Bashir Ahmad inda yace:

“Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatar da shugaban alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen, kuma ya nada  Ibrahim Tanko Muhammed matsayin mukaddashin Alkalin alkalai.”

“Shugaba Buhari ya sallameshi ne bisa ga umurnin kotun hukunta ma’aikatan gwamnati ta CCT”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here