Isah Ahmed Daga Jos
MAKARANTAR koyar da haddar karatun Alkur’ani mai girma ta Madinatul Ahbab da ke garin Kwaftara, kusa da garin Saminaka a Jihar Kaduna, ta yaye daliban da suka sauke Alkura’ani mai girama 74 da dalibai 9 da suka haddace Alkura’ani mai girma, a karshen makon da ya gabata.
Da yake jawabi a wajen taron Imam Hassan Aliyu Sese wanda ya wakilci Sheikh Falalu Dan almajiri ya yabawa daliban, kan kokarin da suka yi, na sauke karatun Alkura’ani mai girma.
Ya yi kira ga daliban su kara zage damtse don cigaba da neman ilmi. Ya ce karatu yanzu kuka fara, don haka ku bada kokari ku cigaba da yin karatu.
Ya yi kira ga al’ummar musulmi su rike Alkura’ani su yi ta karantawa kullum. Ya ce a Aljannah daga Annabawa sai masu haddar Alkura’ani.
Shi ma a nasa jawabin Sheikh Nazifi Ibrahim Zariya cewa ya yi babu wata ni’ima a duniya, da ta kai ni’imar Al’kura’ani.
Ya ce falalar Allah ita ce addinin musulunci kuma ita ce littafin Al’qura’ani mai girma.
Ya ce bayan an sami karatun Al’kura’ani ba a zama, sai a cigaba da neman ilmin fassarar Al’kura’anin.
Tun da farko a nasa jawabin shugaban makarantar Alhaji Adamu Halilu Kwaftara ya bayyana cewa wannan bikin yaye dalibai shi ne karo na 28.
Ya ce a bana sun yaye daliban da suka sauke Alkura’ani guda 74 da daliban da suka haddace Alkura’ani guda 9.
Alhaji Adamu ya yi bayanin cewa daga lokacin da aka vude wannan makaranta, zuwa yanzu sun yaye daliban da suka haddace Alkura’ani mutum 56. Kuma sun yaye daliban da suka sauke mutum 375.
Ya ce baya ga daliban da suke samu a wannan yanki, suna samun dalibai daga wurare daba daban musamman Jihar Kaduna da jihohin Filato da Nasarawa da Kano da Bauchi dai sauransu.
Yace babban abin da suka sanya a gaba shi ne gyara mazaunin wannan makaranta na dindin shekaru 10 da suka gabata.
‘’A duk shekara muna yin noma da kuma taimakon da jama’a suke bayarwa muke amfani wajen kokarin gina mazaunin wannan makaranta.
Don haka muna kira ga al’umma su cigaba da bamu goyan baya da hadin kai ta hanyar taimakawa wannan makaranta, domin mu cimma wannan buri da muka sanya a gaba’’.