An Gano Dalilin Onnoghen Na Dakatar Da Taron NJC

0
725

Daga Usman Nasidi

TSOHON alkalin alkalai na kasa (CJN) Walter Onnoghen, ya dakatar da taron majalisar zartaswa ta shari’ar kasa (NJC) awanni 11 kafin taron ba tare da bayyana wani dalili ba. Sai dai, jaridar SaharaReporters yanzu ta gano dalilin da ya sa ya dauki wannan matakin, wanda baya rasa nasaba da tsoron kar majalisar ta tsige shi.

Majalisar NJC ta gudanar da taronta na 87 a ranar 3 ga watan Oktoba, karkashin jagorancin Onnoghen. A karshe taron, an kawo bukatar nada babban alkali na kotun koli, manyan masu shari’a, da kuma sauran wasu masu shari’ar na manyan kotunan jiha da kuma alkali a kowacce kotun shari’a da kotun daukaka kara da kotun al’adu ta daukaka kara. An shirya gudanar da taron majalisar na 88 a ranar Talata, 15 ga watan Janairu, 2019, wanda Onnoghen ya dage.

Sai dai bayan wasu ‘yan kwanaki, hukumar da’ar ma’aikata (CCB) ta maka alkalin alkalan a kotun da’ar ma’aikata (CCT) kan zarginsa da kin bayyana kadarorin da ya mallaka.

Cike da tsoron cewa majalisar NJC zata dakatar da shi saboda wannan dalilin, Onnoghen, duk da sanin cewa tuni mambobin majalisar suka isa Abuja, ya dakatar da taron har sai baba-ta-gani.

Wata majiya da ke da masaniya akan lamarin, ta bayyana cewa Onnoghen ya dauki wannan matakin ne bayan da lauyoyinsa suka bashi shawara, la’akari da yunkurin da majalisar ke yi na daukar mataki akansa.
Sau biyu dai Onnoghen na kin halartar zaman kotun CCT.

A hannu daya kuwa, babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja da kuma kotun masana’antu, sune suka dakatar da kotun CCT daga ci gaba da sauraron karar.

Sai dai a jiya Juma’a, shugaba Muhammadu Buhari ya sallami shugaban alkalan Najeriya, Jastis Walter Onnoghen kuma ya nada Ibrahi Tanko Muhammad a matsayin mukaddashi.

Majiyarmu ta samu wannan rahoto ne daga bakin hadimin shugaba Buhari kan sabbin kafofin sada zumunta.

Bashir Ahmad inda yace:
“Shugaba Muhammadu Buhari ya dakatad da shugaban alkalan Najeriya, Walter Samuel Nkanu Onnoghen, kuma ya nada Mr Ibrahi Tanko Muhammed matsayin mukaddashin Alkalin alkalai.”

“Shugaba Buhari ya sallameshi ne bisa ga umurnin kotun hukunta ma’aikatan gwamnati CCT.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here