Hadakan Kan Jam’iyyun Adawa Kan Gwamna Bauchi Ba Zasu Sami Nasara Ba – Abdullahi Zabala

  0
  793

  Isah Ahmed Daga Jos

  WANI ma’aikacin gwamnatin Jihar Bauchi mai suna Alhaji Adullahi Sale Bare [Abdullahi Zabala] ya bayyana cewa hadin gwaiwar da jam’iyyun adawa suka yi a Jihar Bauchi, don bugawa da gwamnan Jihar M A Abubakar a  zaben kujerar gwamnan Jihar mai zuwa, ba zasu sami nasara ba. Alhaji Abdullah Sale ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da ‘yan jarida.

  Ya ce maganar hadaka da jam’iyyun adawa suka yi a Jihar Bauchi, don kayar da gwamna M A Abubakar ba zasu kai ga nasara ba. Domin  wannan hadin gwiwa,  hadin gwiwa ne na son zuciya, ba domin talakawan Jihar Bauchi  aka yi ba.

  Ya ce  duk masu fada da gwamna M A Abubakar suna yi ne, don biyan bukatar kansu kuma  gwamna ya ki ya biya masu bukatunsu na son zuciya,  shi ne  yasa suke neman ko ta wanne hali, sai sun ture shi daga kan mulki.

  ‘’Gwamna M A Abubakar  ya shigo da tsari ne kamar na shugaban kasa Muhammadu  Buhari, wajen bin ka’ida. Domin yanzu lokacin da za a rika daukar kudi ana bin ‘yan siyasa gida gida ana raba masu ya wuce. Wannan ita ce matsalar gwamna M A Abubakar da masu adawa da shi. Don haka wannan hadaka ba zata yi wani tasiri ba. Domin ba an yi hadakar don   jama’ar Jihar Bauchi bane. Sun yi ne domin biyan bukatar kan su. Don haka ba zasu sami nasara ba’’.

  Ya ce gwamna M A Abubakar ya yi ayyukan raya kasa da   ya bashi damar  cancantar a sake zabensa karo na biyu, a zabe mai zuwa a Jihar.

  Ya ce babu bangaren jin dadin jama’a  tare  da kyautata rayuwarsu  da bai taba ba.

  Ya ce misali kamar  bangaren hanyoyin mota akwai aikin hanyar Misau zuwa Bulkachuwa wadda   tun zamanin  marigayi tsohon gwamnan Jihar  Abubakar Tatari Ali, mutanen yankunan  suke neman a yi masu  hanyar. Amma babu wanda  ya yi aikin wannan hanya, sai gwamna M A Abubakar.

  Ya  ce yanzu ana nan ana aikin   wannan hanya tun daga Misau ta wuce zuwa Bulkachuwa zuwa Madara har Zaki.  Haka  kuma a Darazo  da Misau da Hardawa  an yi gadoji  ana nan ana aikin yi hanyoyi.

  Ya ce a bangaren ilmi kuma  gwamna M A Abubakar ya yi qoqari ana nan ana ta gyare gyaren makarantun sakandire da firamare a Jihar. Kuma  an sayi litattafan karatu da rubutu an rarrabawa  makarantun Jihar.

  Ya ce a banagaren kiwon lafiya kuma  da hawan gwamna M A Abubakar  ya gina sababbin asibitoci a dukkan kananan Hukumomin Jihar  20. Kuma  an zuba kayayyakin aiki da magunguna a wadannan asibitoci.

  Alhaji Abdullahi Sale ya yai bayanin cewa a duk gwamnonin da aka yi a Jihar Bauchi, babu gwamnan da yake kula da biyan ma’aikata albashi kamar gwamna M A Abubakar. Ya ce  yanzu a duk  ranar 23 zuwa 25 na kowanne wata ake biyan ma’aikata albashi, a Jihar Bauchi. Ko an sami kudi daga asusun tarayya ko ba a samu ba, haka gwamna M A Abubakar yake biyan ma’aikatan Jihar albashinsu.

  Ya ce duk da gwamna M A Abubakar ya samu an dauki ma’aikata sama da dubu 100 a Jihar  an saka su a tsarin biyan albashi, amma ba a fara biyansu ba. Wadansu  suna bin albashi na sama da shekara,  amma zuwan gwamna M A Abubakar ya biya wadannan ma’aikata dukkan  basussukan albashi da suke bi.

  Ya yi Kira ga al’ummar Jihar Bauchi  su fito kwasu da kwarkwatarsu su sake zaben gwamna M A Abubakar a Jihar.  Kuma su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari, domin su cigaba da kudurorin da suka sanya a gaba

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here