Isah Ahmed Daga Jos
WANI matashi dan shekaru 25 da ya fito takarar kujerar majalisar dokoki ta Jihar Filato, a mazabar Jos ta Arewa maso Arewa karkashin jam’iyyar Democratic Alternative D A, Kwamared Haruna Yusuf Abba ya bayyana cewa matasa ne, suka fara kawo cigaba a Najeriya. Kwamared Haruna Yusuf ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.
Ya ce sau tari mutanen Najeriya suna duban shekaru ne, amma idan aka lura matasa ne suka fara kawo cigaba a Najeriya. Ya ce yawaicin shugabanninmu na baya a Najeriya, wasu sun yi shugabancin ne suna da shekaru 22 zuwa 27 ne. Kuma sun sami nasarar kawowa Najeriya gagarumin cigaba, da har yanzu muke cin gajiyarsu a Najeriya.
Ya ce idan har wadannan shugabanni sun sami nasara a lokacin da suka yi shugabanci, lokacin da babu ilmi maye zai hana matasa su yi nasara a wannan zamani da ilmi ya yi yawa?.
Ya ce don haka idan aka baiwa matasa dama a wannan lokaci, da yardar Allah zasu yi abubuwan da zasu kawo cigaba a Najeriya.
‘’Yanzu idan ka dubi wasu kasashe da suka cigaba a duniya yawaici matasa ne, suke mulkin wadannan kasashe. Kuma suna samun nasara, saboda matashi ne yake da karfin jiki. Idan har yanzu a Najeriya, sai dai ace matasa su je su jefa kuri’a ne kawai, su zabi wadanda ba zasu taimaka masu ba. To babu wani cigaba ga matasa a siyasar Najeriya’’.
Kwamared Haruna Yusuf ya yi bayanin cewa babban abin da ya karfafa masa gwiwar fitowa wannan takara, shi ne don ya bada gudunmawarsa a matsayisa na matashi.
Ya ce tun da aka dawo mulkin damakoradiya a shekara ta 1999 har zuwa yanzu babu wani abu na cigaba, da aka yi a wannan mazaba.
Ya ce al’ummar wannan mazaba suna fama da matsalolin na rashin ruwan sha da rashin kujeru da kayan aiki a makarantun gwamnati da rashin dakunan shan magani da kananan asibitoci da rashin aikin yi ga matasa da rashin tallafawa mata masu sana’o’i a gidajensu a wannan mazaba.
Ya ce idan Allah yasa ya yi nasara, zai yi amfani da kudaden da ake warewa mazabu don warware wadannan matsaloli da suke damun wannan mazaba.
Ya yi kira ga al’ummar mazaba su fito su kwansu da kwarkwatarsu su zabi mutumin da ya dace kuma ya cancanta a zaben da za a gudanar.