Buhari Ya Kaddamar Da Hakar Man Fetur A Tsakanin Bauchi Da Gombe

0
1201

Daga Usman Nasidi

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da fara hakan/tonon iskar gas, da danyen man fetur na Kolmani da ke karamar hukumar Alkeri da ke jihar Bauchi.

Da ya ke kaddamar da hakar man a kauyen Burumbu da ke karamar hukumar Alkaleri, shugaban kasa Buhari ya yi nuni da cewa iskar gas da danyen mai har yanzu sune manyan bangarorin da kasar ke samun kudaden kaddamar da kasafin kasar da kuma habbaka tattalin arziki.

Shugaban kasar ya bayyana cewa ya dauki sha’awar fadada bincike kan samar da man fetur a lokacin da yake rike da mukamin kwamishinan albarkatun kasa na tarayya a 1960, amma cikin rashin dace, aka dakatar da hakan bayan shekaru biyu, a lokacin mulkin Obasanjo.

Ya yi amfani da damar wajen yin godiya ga kamfanin NNPC bisa namijin kokarinsu na ganin aikin hakar mai a wajen ya kankama cikin kankanin lokaci.

Tun farko, gwamnan jihar Bauchi Mumammad Abdullahi Abubakar ya bayyana jin dadinsa kan yadda har aikin hakar mai a jihar ya kai wannan matsayi, tare da jinjinawa shugaban kasa Buhari na fara assasa aikin.

Babban daraktan NNPC, Dakta Maikanti Baru ya ce NNPC tare da hadin guiwar wani kamfanin kasar China sun gano man fetur da iskar gas mai yawa a garin, domin haka ne ya bayyana bukatar gaggauta fara hakar ma’adanan.

Shugaban kasar ya samu rakiyar gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abubakar, tare da takwaransa na jihar Gombe, Ibrahim Dankwambo, ministoci da kuma manyan jami’an gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here