Ahmed Garba Bichi Zai Kawo Sauyi A Kano Ta Arewa – Kungiyar Matasa

  0
  2056

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano

  WATA kungiya ta matasa dake mazabar dan majalisar dattijai ta kano ta arewa  mai suna “Kungiyar samar da canjin wakilci a kano ta arewa” ,ta bayyana cewa Ahmed Garba Bichi shi ne zai kawo managarcin sauyi a wannan mazaba saboda ingancin sa.

  Kungiyar matasan tayi wannan tsokaci ne cikin wata zantawa da tayi da wakilin mu a karahen wani taro na matasan yankin domin fara zagayen kananan hukumomi 13 na wannan shiyya dangane da bukatar sauyin wakilcin mazabar.

  Mai magana da yawun kungiyar  Malam Auwal Usman Waddau daga karamar hukumar Dawakin Tofa yace mazabar kano ta arewa bata yi dacen wakili ba a majalisar dattawa, sannan itace koma baya a dukkanin mazabun majalisar ta dattawa dake jihar kano wanda kuma hakan  abin takaici ne matuka.

  Auwal Usaman ya kara da cewa muddin anaso a sami ci gaba a wannan mazaba, lallai sai an sami canjin wakili wanda yasan makamar aiki tareda sanin matsalolin wannan shiyya ta kano ta arewa, wanda bisa hakane suka kafa wannan kungiya domin ganin an sami wakilci na adalci sabanin halin da ake ciki a yau.

  Yace yanzu matasan kano ta arewa suna da kungiyoyi masu tarin yawa, wadanda duka manufofin su daya ne, watau samun canjin wakilci a yankin, wanda kuma a cewarsa, Ahmed Garba Bichi shine wanda aka hakikance zai yi aiki bisa gaskiya da amana idan aka zabe shi a matsayin sanatan kano ta arewa.

  Bisa hakane kungiyar ta bada sanarwar cewa zata fara kai ziyarar ankarar wa ga matasan kano ta arewa tareda fayyace irin alheein dake tattare da zaben Alhaji Ahmed Garba a matsayin sanatan mazabar domin gani an sami ribar dimokuradiyya  mai amfani.

  A karshe, matasan sun nunar da cewa zaben Ahmed Garba shine mafita a shiyyar kano ta arewa sannan al’umar wannan mazaba zasu rabauta sosai daga wakilcin da zai yi domin ana ganin abubuwan da yake yi a mazabarsa ta dan majalisar wakilai tun da aka tura shi.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here