Ana Zargin Yin Magudi A Zaben Jihar Kaduna Mai Zuwa – Dan Takarar APGA

  0
  791

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  DAN takarar gwamnan Jihar Kaduna Karkashin jam’iyyar APGA mai alamar zakara Dakta Polycarp GanKon ya bayyana cewa da akwai alamun da ke nuni da cewa ana kokarin yin zaben magudi a zabe mai zuwa don haka yake kokarin fadakar da hukumar zabe da kuma daukacin al’umma baki daya domin tabbbatar da yin gyara kafin zaben mai zuwa.

  Dakta Polycarp Gankon ya bayyana hakanne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a cibiyarsu da ke kaduna, inda ya ce hakika batun da hukumar zaben ta yi na cewa ta kirkiro karin wadansu mazabu har guda dubu Takwas wani al’amari ne mai ban tsoro domin ya dace a fayyace wa jama’a wuraren da aka kara wadannan mazabu ta yadda kowa zai fahimci abin da ake nufi da kuma wuraren baki daya.

  (Hakika abin da hukumar zaben ta aiwatar yana da matukar muhimmanci saboda akwai wuraren da akwatunan zabe ne amma sun wuce ka’aidar mutane dari biyar a kowa ne akwati kamar yadda tsarin zabe ya tanadar, domin zaka ga akwatuna na kaiwa dari takwas,Tara har dubu da wani abu,don haka karin mazabun yana da kyau.Amma batun sh ne an kasa fadin wuraren da aka kara wadannan akwatunan zaben, wanda ko a haka ana iya yin magudin zabe da sunan a kara wuraren yin zabe wato Tashoshin zabe amma babbar matsalar shi ne jama’a ba su sani ba sam,dole ne hukumar zabe ta tashi tsaye domin yi wa jama’a bayani).

  Dakta Polucarp, ya kuma karyata batun da yan batanci ke kokarin yada wa cewa wai shi yana da tsananin addini,ta yaya zaka ce mutum na da tsananin addini bayan kuma ba haka ba ne ni a yanzu a cikin gida na ina da wani yaro daga shika yake yana karatu a jami’ar Ahmadu Bello Zariya sunansa (Idris Jamilu)

  “Ni nake biyan kudin makarantarsa kuma a cikin gida na yake babu wani bambanci da dan da na haifa ko abinci ne ba wanda zai saka masa abinci a kwano sai dai shi ya zuba wa kansa duk abin da zai ci kamar kowa, nan yake kwana baki daya a gida na yake, to, ta yaya wani zai ce ina da bambanci? kuma na horar da yara har mutum biyu irin aikin da nake yi a da can mutanen nan da na ke tare da su duk musulmai ne kuma a yanzu duk sun zama wani abu a rayuwa duk daga karkashina, wannan kadan kenan”.

  Ya kuma shaidawa manema labarai cewa shi a matsayinsa n adan Jihar kaduna ya fito ne domin canza al’amura ta yadda komai zai yi aiki kamar yadda ya dace ba irin canjin da ake yayatawa ba kawai.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here