Zamu Ci Gaba Da Wayar Da Kan Mata AKan Su Zabi Buhari – Inji Mataimakiyar Shugabar BCO

  0
  724

  JABIRU A HASSAN, Daga Kano

  MATAIMAKIYAR shugabar mata ta kungiyar yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari watau BCO, ta shiyyar arewa maso yammacin kasarnan, Hajiya Halima Ben Umar tace kungiyarsu zata ci gaba da wayar da kan mata dangane da yadda zasu zabi shugaba Buhari kamar yadda ake bukata.

  Tayi wanna bayani ne cikin hirar da suka yi da wakilinmu a kano, inda tace ko shakka babu, kungiyar BCO tana aiki tukuru domin ganin an sake zabar Buhari a matsayin shugaban kasa karo na biyu ta yadda kasar nan zata sami ci gaba mai albarka.

  Halima Ben Umar tace matan kasar nan zasu kara samun ci gaba idan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake cin zabe karo na biyu, domin a cewarta, Buhari mutun ne mai kyawawan manufofi na bunkasa kasarnan da daukacin al’umar ta bisa la’akari da bukatun kowane bangare.

  Ta nunar da cewa kungiyar su ta BCO ta hakikance cewa idan Buhari ya yi shekaru takwas a matsayin shugaban kasarnan, babu shakka za’a ga ci gaba mai amfani a birane da yankunan karkara, don haka ne ma suke aiki dare da rana domin ganin shugaban ya sami nasarar cin zabe ta yadda zai dora kasarnan bisa ginshiki mai inganci.

  Hajiya Halima ta bada tabbacin cewa aikin da kungiyar BCO keyi zai taimaka wajen tabbatar da samun nasarar jam’iyyar APC da shugaba Muhammadu Buhari musamman ganin cewa gwamnatin sa tana sanya su cikin shirye-shiryenta kamar yadda ake bukata.

  Daga karshe, tayi amfani da wannan dama wajen yabawa uwargidan shugaban hukumar kula da kafafen sadarwa watau NCC,  Dokta Halima U.D Dambatta saboda tallafawa shirin wayar da kan mata da kungiyar ta BCO keyi, tareda bada magunguna kyauta ga mata da kuma basu jari batareda nuna gajiyawa ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here