Aminu Goro Ya Cancanci Komawa Majalisa – Inji Usman Dan Gwari

  0
  947
  JABIRU A HASSAN, Daga, Kano

  WANI jigon jam’iyyar APC a jihar Kano, Alhaji Usman Dan Gwari ya nuna gamsuwar sa bisa  yadda wakilin karamar hukumar Fagge na majalisar wakilai ta tarayya, Kwamared Aminu Sulaiman Goro ya gudanar  da wakilcin al’uma tun  da  aka zabeshi a matsayin wakilin mazabar.

  Yayi wannan bayani ne a hirar da suka yi da wakilin mu a kano, inda ya sanar da cewa  ko shakka babu, Aminu Goro ya cancanci a sake zaben sa Karo na uku saboda wakilci na adalci  da yake  yi batare  da nuna bambancin siyasa ko na ra’ayi ba, wanda  hakan ake  bukata daga  shugaba nagari.

  Alhaji Usman Dan Gwari ya ce “dan majalisa Aminu Goro ya Samar da abubuwa na more rayuwa masu dumbin yawa a fadin karamar hukumar Fagge wadanda kuma za’a dade  ana  amfanar su wanda  lokaci bazai bari  a bayyana su duka ba saboda yawansu a kowane fanni na kyautatuwar zamantakewar al’uma.”

  Sannan ya sanar da  cewa al’umar karamar hukumar Fagge shaida ne  kan abubuwa na alheri da  Kwamared Aminu Goro ya gudanar a yankin, inda kuma kowace mazaba ta rabauta da  aikace-aikace maau amfani kamar yadda ake  gani a ko’ina duk  da cewa aikin dan majalisa  shine yin doka kamar yadda tsarin aikin su ya tanada.

  Alhaji Usman Dan Gwari ya yi albishir cewa dan  majalisa Aminu Goro zai rubanya kokarin sa wajen samarda aiyukan raya kasa data gwamnatin tarayya idan aka sake zaben sa zuwa majalisar wakilai musamman ganin iron kokarin da yayi aka gani tun farkon turashi a shekara ta 2011.

  A karshe, Dan Gwari yayi Kira ga daukacin al’umar karamar hukumar Fagge dasu sake baiwa Aminu Goro dama domin ci gaba da wakilcin da take yiwa wannan mazaba, tareda fatan cewà za’a zabi jam’iyyar APC daga sama had kasa saboda kyawawan manufofin ta ga al’umar kasa baki daya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here