Akwai Matsala A Runfuna Kimanin 24 A Jihar Yobe – Inji Hukumar Zabe

0
810

Muhammad Sani Chinade Daga Damaturu

HUKUMAR zabe mai zaman kan ta a Nijeriya (INEC), rashen jihar Yobe ta bayyana cewa a bisa dalilin tabarbarewar tsaron da ya yi kamari a kwanakin nan za a iya fuskantar matsala a cibiyoyin jefa kuri’a 24 a jihar a wannan babban zabe na kasa dake tafe.

Shugaban hukumar rashen jihar Yobe, Ahmadu Makama ne ya bayyana hakan ga uwar kungiyar ‘yan jaridu  NUJ ta kasa a reshen Jihar Yobe, a sa’ilin da shugabannin kungiyar suka kai ziyara a cibiyar hukumar ta INEC da ke Damaturu.

Ya bayyana cewar akwai kimanin cibiyoyin jefa kuri’a guda 24 wadanda zai yi matukar wahala a iya gudanar da zabe a cikin su, wanda hatta ‘yan asalin yankin abin ya gagare su ballantana kuma hukumar INEC; saboda haka ba za a jefa jama’a cikin hatsari ba.

Ya ce “har yanzu akwai katin zabe kimanin dubu dari wadanda masu shi basu zo sun karba ba.”

“yanzu haka muna ajiye da dandazon katin zaben da ba a karba ba a nan jihar Yobe.”

Da yake maganar alakar hukumar da ‘yan jaridu a jihar, shugaban hukumar zaben ya roki manema labarai a jihar da cewa su hada hannu da karfe hukumar wajen ganin manyan zabubbuka masu zuwa sun gudana a cikin nasara.

Acewarsa, a kowanne lokaci kofar su a bude ta ke wajen yada ingantattun bayanai wadanda zasu taimaka musu wajen wayar da kan jama’a, kuma yana mai bada tabbacin zanta wa dasu domin gaya wa jama’ar Yobe da kasa baki daya dangane da aikace-aikacen wannan hukuma tasu.

A nashi bayanin, shugaban gamayyar kungiyar manema labaru rashen jihar Yobe (NUJ) Yusuf Alhaji Isa, ya bayyana cewa kungiyar tana da bangarori takwas wadanda ke aiki a karkashin ta.

Ya ce “kamar yadda manyan zabuka ke karatowa, a shirye muke wajen hada hannu wuri guda tare da wannan hukuma ta INEC wanda idan za a tuna, a zabubbukan 2015, mun bayar da gagarumar gudumawa wajen samun nasara”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here