Dalilan Da Suka Sa Zamu Sake Zaben Sanata Kabiru Gaya

  0
  1189

  Mustapha Imranà Abdullahi

  WADANSU gamayyar masu aikin fadakar da al’umma musamman game da harkokin siyasa da ke amsa sunan masu wayar da jama’a daga Shiyyar  Kano ta Kudu (Political awareness group, Kano South Awareness Forum )(KSAF) sun bayar da dalilan da yasa suke kokarin goyon bayan sake zaben Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, domin ci gaba da wakiltar mutanen Kano ta Kudu a majalisar Dattawa ta kasa.

  Gamayyar kungiyoyin sun ce suna ta fafutukar yin Yakin Neman Zabe domin ganin sanatan ya sake lashe zaben da ke tafe a nan da yan kwanaki masu zuwa ne domin nagartarsa.

  Shugaban gamayyar yan fafutukar, Alhaji Idris Kachako, ya shaidawa manema labarai cewa tun bayan da shugaban Jam’iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya Mika tuta ga Sanata Kabiru Gaya a matsayin wanda zai tsayawa Jam’iyyar takara a ranar 16 ga watan Fabrairu a filin wasa na Sani Abacha da ke cikin garin Kano, tun daga nan ma jama’a suka sakankace cewa lallai ayyukan da Sanatan ya aikwatar sun isa tabbacin ya samu cikakken goyon baya da duk wani hadin Kai daga al’ummar Kano ta Kudu baki daya.

  Idris Kachako ya ci gaba da bayar da misalin cewa ayyukan Sanata Kabiru Gaya suna nan a kowa ne Sako da lungu na mazabar Kano ta Kudu har ma da wadansu makwabtansu ma sun samu ribar wakilcinsa a majalisar Dattawa ta kasa. Kuma wannan tsari da tsohon Gwamnan Jihar Kano ke yi ya bayar da dama ga jama’a su san cewa shi ne Dan Majalisar Dattawan da yaje majalisa domin kare hakkin jama’a baki daya.

  ” Wannan ne karo na farko da aka nada wani daga arewacin Nijeriya a majalisar Dattawa ya zama shugaban kwamitin ayyuka wanda hakan ya bayar da dama ake ta Gina Tituna a yankin Kano ta tsakiya da kuma daukacin arewacin kasar baki daya.

  Kachako ya kara da bayar da wani misalin cancantar Kabiru Gaya da cewa ya gabatar da kudirin a samar da wata hukumar da za ta kula da yankin Arewa maso Gabas (NEDC), wannan al’amarin ne da ba za a mance shi cikin sauri ba.

  “Kuma Sanata Kabiru Gaya shi ne ya zama Dan majalisa na farko daga Nijeriya da aka zaba a matsayin Mataimakin shugaban kungiyar yan majalisa na kasa da kasa ( IPU).

  Bisa irin wadannan abubuwan da suke fitar da Nagartar Sanata Kabiru Ibrahim Gaya shi ne mutumin da ya dace a zaba a matsayin wakilin Kano ta Kudu, saboda haka ne wannan kungiya da muka ambata a sama suke kira ga wasu yan takarar da suke neman wannan kujerar da su hanzarta sauka daga matsayin takara da sanata Gaya, tun kafin ranar zabe domin dukkan alamu sun tabbatar cewa babu wanda jama’a za su zaba Sai tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata a yanzu Kabiru Ibrahim Gaya.

  Ya kuma bayar da shawara ga sauran yan takarar da su duba wadannan nasarorin da Sanata Gaya ya Samar wa jama’a a ciki da wajen Jihar Kano tare da kasa baki daya su yi abin da ya dace kafin lokaci ya kure.

  Alhaji Kachako ya kuma yi kira ga jama’ar Kano ta Kudu da su yi tururuwar fitowa a ranar zabe domin ba Sanata Kabiru Ibrahim Gaya kuri’ar da ta wuce wadda suka bashi a zaben shekarar 2015.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here