Kungiyar Malaman Jami’o’i Ta ASUU, Sun Janye Yakin Aiki

0
748

Daga Usman Nasidi

A RANAR Alhamis ne kungiyar malaman jami’o’i ta sanar da janye yajin aikin da ta dauki tsawon watanni uku ta na yi.

Shugaban kungiyar na kasa, Farfesa Biodun Ogunyemi, ne ya sanar da janye yajin aikin yayin wata ganawa da manema labarai a Abuja, birnin tarayya.

Kungiyar ta janye yajin aikin ne bayan wata gana wa da wakilan gwamnatin tarayya da ministan kwadago da samar da aiyuka, Sanata Chris Ngige, ya jagoranta.

ASUU ta ce ta janye yajin aikin ne bayan kamala tuntuba da tattauna wa a kan tayin da gwamnatin ta yi a kan bukatun da kungiyar ta bukaci a cika ma ta kafin ta koma bakin aiki.

A sanarwar da ta fitar, ASU ta ce bayan amince wa da gwmnatin tarayya ta yi na sakin biliyan N20 domin biyan malaman jami’o’I bashin alawus da su ke bi a shekarar 2018, gwamnatin ta yi alkawarin sake fitar da wata biliyan N25bn a watan Afrilu zuwa Mayu na shekarar nan, bayan haka kuma gwamnatin za ta cigaba da zartar da yarjejeniyar da su ka kulla da ASUU tun shekarar 2013.

ASUU ta yi godiya ga kungiyoyi daban-daban, musamman kungiyar kwadago, bisa goyon baya da hadin kan da su ka ba su yayin yajin aikin.

Kazalika, kungiyar ta ASUU ta yi Alla-wadai da halayyar wasu shugabannin jami’o’in kasar bisa yunkurin yin kafar angulu ga yajin aikin.

ASUU ta shiga yajin aiki ne tun watan Nuwamba na shekarar 2018 bayan ta zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula a kan bangaren ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here