Masaurautar Pataskum Ta Nada Jakadan Najeriya A Kasar Sudan A Matsayin Wakilin Ta

0
928

SANI GAZAS CHINADE DAGA DAMATURU

MAI Martaba Sarkin Potiskum na jihar Yobe, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya nada jakadan Nijiriya a kasar Sudan, Ambasada Musa Mamman Saban, a matsayin (sarautar) Wakilin Pataskum, saboda yadda yake bayar da gudummawarsa dangane da ci gaban
masarautar da ma jihar baki daya.

Bikin nada basaraken gargajiyar, ya samu halartar gwamnan jihar Yobe, Alhaji Ibrahim Gaidam wanda sakataren gwamnatin jihar- Baba Malam Wali ya wakilta tare da sauran manyan mutane wadanda suka zo, ciki da wajen kasar nan.

Jim kadan da nada wa Musa Mamman rawanin, Sarkin Potiskum ya bayyana cewa, masarautar Potiskum ta yanke shawarar nada shi ‘Wakilin Potiskum’ ne bayan tuntuba da lura wanda ta gudanar dangane da cancantar jekadan a wannan matsayi.

An haifi Ambasado Musa Mamman Saban, ne a garin Potiskum a shekarar 1967, wanda ya gudanar da karatun sa kama daga firamari, sakandare a tsakanin mahaifar sa zuwa Borno College of Education da Science and Technology, da ke garin Bama a tsohuwar Jihar Borno.

Bugu da kari, wakilin na Pataskum ya samu damar zarcewa zuwa jami’ar Maiduguri a (1988-1991) inda ya yi digirin sa na farko, sai jami’ar Nkumba, Etembe, a kasar Uganda 2003-2005, digiri na biyu.

Jakadan Musa Mamman, ya fara aiki a ma’aikatar kula da kasashen waje da ke Abuja, sannan daga bisani aka nada shi jekadan Nijeriya a Hawa, da ke kasar Kanada a 1998 zuwa 2000.

Har wayau ya rike matsayin Wakilin Nijeriya a kasashen Kampala, Uganda da kasar Togo sai kuma kasar Zimbabwe, kana babban jami’im hulda a tsakanin Nijeriya da Saudi Arabiya- Jedda, kana daga bisani zuwa Khartoum, ta kasar Sudan.

Da yake bayyana farin cikin sa dangane da sarautar ‘Wakilin Potiskum’, Ambasada Musa Mamman Saban ya nuna matukar godiyar sa ga masarautar Potiskum tare da al’ummar ta, da jihar Yobe baki daya bisa wannan karamma wa da kaunar da suka nuna masa, wanda ya bayyana a matsayin
gagarumar nasara a rayuwar sa.

Ya yi alkawarin wajen ci gaba da bayar da goyon baya a ci gaban jama’ar Yobe baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here