VGN Zata Yi Kokarin Hana Rikice – Rikice Lokacin Zabuka – Inji Muktar Ungogo

0
985

JABIRU A HASSAN, Daga, Kano

AN bayyana cewa kungiyar tsaro ta sakai watau Vigilante group of Nigeria (VGN) zata ci gaba da kokarin hana aukuwar rikice-rikice lokutan zabe da kuma bayan gudanar da zabuka maau zuwa.

Wannan tsokaci ya fito ne daga jami’in tattara bayanai na kungiyar Muktar Abdullahi Ungogo, a tattaunawar su da wakilin mu, inda yace kungiyar ta VGN tana aiki ne domin tallafawa hukumomin tsaro wajen gudanar da aiyukan su na tsaron lafiya da dukiyoyin al’uma a birane da yankunan karkara.

Yace a wasu lokutan, VGN tana dakile aukuwar wasu abubuwa da ke faruwa wadanda kuma suke bukatar gwamnati ta kara daukar matakai a kanau ta yadda zaman lafiya zai bunkasa zaman lafiya a fadin kasa.

Haka kuma ya sanar da cewa yanzu kungiyar VGN tana kara bunkasa musamman ganin yadda ake cire batagari daga cikin ta, tareda kyautata yanayinta ta yadda zata  ci gaba da tallafawa hukumomin tsaro wajen kare martabar kasarnan .

Daga karshe ya roki gwamnatin tarayya data samar da motoci da sauran kayan aiki ga kungiyar ta VGN, tareda jinjinawa babban kwamandan kungiyar, Alhaji Ali Sakkwato da daukacin yayan kungiyar, wadanda suka sadaukar da kansu domin gyaran kasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here