Ba A Isa Ayi Zabe A Zamfara Ba Idan Har Aka Cire APC – Gwamna Yari

0
830

Daga Usman Nasidi

GWAMNA Abdul’Aziz Yari Abubakar na jihar Zamfara ya yi barazaar cewa babu zaben da za a yi a jihar idan har hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta cire yan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) daga cikin zaben kasar mai zuwa.

Gwamna Yari ya bayyaa hakan a ranar Juma’a, 8 ga wata Fabrairu lokacin gangamin jam’iyyar APC a karamar hukumar Talata Mafara a ci gaba da gangamin zabensa a ke gudana a jihar.

“Babu yadda za a yi a gudanar da zabe a jihar Zamfara ba tare da yan takarar APC ba, duk da hukuncin babbar kotun Zamfara da ta tabbatar da cewar APC ta gudanar da zaben fidda gwani a jihar”, Yari yayi gargadi.

Yace haka zai zamo babban kuskure da barazana ga tsaron kasa idan har hukumar INEC ta hana yan takarar APC a Zamfara takara a lokacin zabe mai zuwa a jihar.

Yari ya bukaci masu zabe da su zabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkanin yan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

Hukumar INEC na kan bakarta na cewa APC reshen Zamfara bata da yan takara saboda jam’iyyar bata gudanar da zaben fidda gwani ba sannan bata gabatar da jerin sunaye ga hukumar ba a ranar 7 ga watan Oktoba wanda shi ne ranar karshe da hukumar ta bayar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here