Diyar Buba Galadima Ta Halarci Taron Gangamin Kamfe Din Buhari Na Legas

  0
  783

  Daga Usman Nasidi

  A WANI yanayi mai kama da maganar nan ta Hausawa da ake cewa ‘in ka haifi mutum, baka haifi halin sa ba, an ga diyar fitaccen dan adawar nan na Shugaba Buhari a yanzu kuma tsohon aminin sa a siyasance, Injiniya Buba Galadima a taron gangamin kamfe din Buhari na jihar Legas.

  Zuwan na Zainab Buba Galadima dai yayi ta jawo cece kuce tare da tayar da kura musamman ma a kafafen sadarwar zamani tun bayan bullar hoton ta tare da mai magana da yawun kwamitin kamfe din yakin neman zaben Shugaba Buhari, Festus Keyamo.

  Rahotanni sun bayyana cewar mutane dai na maganar cewa kamar akwai darasi babba a cikin hakan musamman ma ganin yadda shi mahaifin nata ke zaman na gaba-gaba wajen adawa da shugaba Muhammadu Buhari daga bangaren Atiku Abubakar.

  Ita dai diyar ta Injiniya Buba Galadima kamar yadda muka samu tana aiki ne a fadar shugaban kasar na Najeriya kuma tana goyon bayan sa duk kuwa da matsayar mahaifin ta a kan hakan.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here