Fulani Makiyaya Ba Zasu Taba Amincewa Dokar Hana Kiwo A Najeriya Ba- Gan Allah

0
789

 Isah Ahmed Daga Jos

Kungiyar cigaban al’ummar Fulani ta Nijeriya ta Gan Allah ta bayyana cewa al’ummar Fulani makiyaya na Najeriya, ba zasu taba amincewa da kafa dokar hana kiwo a Najeriya ba. Kungiyar ta bayyana haka ne a takardar sanarwar bayan taron ta na kasa, da ta gudanar a garin Kaduna.

Da yake karanta takardar sanarwar bayan taron,  shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Sale Bayari ya bayyana cewa kamar yadda  kowa ya sani ne tsarin mulkin Najeriya, ya baiwa kowanne dan Najeriya yanci yayi walwala ya shiga duk inda yaga dama a Najeriya.

Ya ce amma don raina hankalin mutane, sai yau aka wari gari aka ce wai wasu Jihohi a Najeriya, sun  kafa dokar hana Fulani kiwo.

‘’Bafulani bai taba tunanin cewa wata rana za a hana shi kiwo a Najeriya ba. Bafulatani bai san wata sana’a ba, sai kiwon dabbobinsa don haka babu abin da yake so, sai dai a bar shi ya cigaba da kiwon dabbobinsa a daji da ya gada daga iyaye da kakaninsa’’.

Alhaji Bayari ya yi bayanin cewa duk wanda ya kawo shawarar a hana Fulani kiwo a Najeriya yana kokarin hallaka al’ummar Fulani ne. Kuma al’ummar Fulani ba zasu tsayawa suna kallon a hallaka su ba.

Ya ce idan  ana son a zauna da al’ummar Fulani lafiya a Najeriya a bar  su yi sana’ar  da suka gada daga iyaye da kakanni.

‘’ Zasu cigaba da yaki kan wannan doka ta hana kiwo, da wasu Jihohi suka kafa Najeriya. Hadari ne gwamnatin Najeriya ta bar wata Jiha ta kafa dokar hana kiwo a Najeriya’’.

Ya ce muna gayawa gwamnati idan ba zata tsare mu ba, zamu tsare kanmu. Domin dokar Najeriya da dokar majalisar xin duniya  ta baiwa kowanne dan Najeriya hurumin ya kare kansa idan har gwamnati ta gaza kare shi.

Ya ce gwamnatin Najeriya bata kare al’ummar Fulani ba. Don haka muna gayawa gwamnatin Najeriya ta kare al’ummar Fulani.

Ya ce  yau rikici tsakani Fulani makiyaya da manoma ya cinye dabbobin Fulani kashi 35 cikin 100.

Ya ce  duk tallafin da gwamnatin Najeriya take yiwa manoma bata taba tallafawa Fulani makiyaya ba.

Ya ce a Najeriya  kowace rana ana cin dubban shanun da Fulani makiyaya suke samarwa. Badan shanun da Fulani makiyaya suke sanarwa a Najeriya ba, da sai gwamnati ta dauki biliyoyin naira ta kashe wajen shigo da shanu a Najeriya.

Ya ce gwamnatin Najeriya ta tallafawa manoman da suka yi asara sakamakon ambaliyar ruwan da aka yi a shekarar da ta gabata da kudi, naira biliyan 84. Haka kuma ta tallafawa manoman shinkafa da kudi naira biliyan 60.

Ya ce   cikin shekaru 3 da suka gabata Fulani makiyaya  sun yi asarar mutane sama da  2700 da shanu sama da miliyan 3, a  Jihohin Taraba da Benuwai da Filato da kudancin Kaduna da Kwara da Kogi da Zamfara da Sakkwato da Katsina.  Amma babu wata gwamnati ta Karamar Hukuma ko  Jihar Ko  Tarayya da ta tallafawa al’ummar Fulani kan wannan asara da suka yi.

Ya ce   yau  ‘yayan Fulani sama da 3000 ne   suke tsare a gidajen kurkuku da ofisoshin ‘yan sanda a Najeriya. Ya ce shekaru 20 da suka gabata babu yaran Fulani 300 a gidajen kurkuku. Saboda ba a hana su sana’ar da suka gada daga iyaye da kakanni ba.

Ya ce suna  kira ga gwamnatin Najeriya ta yiwa ‘yayan Fulani makiyaya da suke tsare a gidaje kurkukun kasar nan ahuwa, kamar yadda aka yiwa ‘yan Neja Delta.

Ya ce al’ummar Fulani makiyaya na Najeriya wadanda suka kai miliyan 25, suna son ayi taron  gyara fasalin Najeriya. Ya ce yin wannan taron  zai baiwa al’ummar Fulani da sauran al’ummomin Najeriya damar  bayyana abubuwan da suke so.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here