Gwamnan Zamfara Na Yawon Tallar Dan Takarar Bogi – Marafa

  0
  1122

  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

  GAMAYYAR yan takarar Gwamnan Jihar Zamfara karkashin Jam’iyyar APC sun bayyana wa manema labarai a kaduna cewa Yawon Tallar Dan takarar Gwamna da Abdul’aziz Yari Abubakar yake yi ya sabawa dokar kotu da kuma ta Jam’iyyar APC.

  Gamayyar hadin Gwiwar Yan takarar su Takwas sun shaidawa manema labarai a kaduna cewa irin yadda Gwamna Yari ke yawo da sunan yana yakin neman zabe ya sabawa dokar jam’iyya da kuma abin da kotu ta bayyana game da dambarwar da ke faruwa a tsakanin su yan takara da kuma mutumin da Gwamna ke Goyawa baya.

  Kamar yadda Mai magana da yawun gamayyar ya ce”ta Yaya Gwamna zai zauna haka kawai ya fadi sunan Dan takarar jam’iyya ya Mika shi a matsayin Dan takara, bayan ga abin da kotu ta ce Amma Gwamnan Zamfara Yari haka kawai ya sabawa doka”. Inji sanata Marafa.

  Koda yake Muna da yakinin cewa hukumar zabe ta kasa karkashin Furofesa Mahmud Yakubu na nan a kan matsayin ta na ba a yi zaben fitar da Gwani ba a Jihar Zamfara karkashin APC ba kamar yadda suka bayar da shaida a gaban kotu.

  Bisa dalilan da muke da su ba shakka Muna da tabbacin cewa Tallar Dan takara na haramun ba Abu ne Mai yuwuwa ba, domin komi Dade wa gaskiya za ta tabbata.

  “Koda yake kamar yadda Gwamna Abdul’aziz Yari yake magana tamkar yana ganin shi ya Fi karfin kowa ne Ko kuma zai iya sauran kowa”, inji sanata Marafa.

  Ya ci gaba da cewa irin yadda Gwamna Yari ke gudanar da lamarinsa yana yi kamar shi ba mutum ba ne, ” Domin yaje karamar hukuma ta da sunan Yakin Neman Zabe Tare da Dan takarar bogi, Amma ya kasa zuwa kauyen da aka kashe Yar uwata ya yi masu jaje duk da cewa Bai wuce Nisan kilomita Goma ba daga inda yake zuwa kauyen”, kamar yadda sanata Marafa ya fayyacewa manema labarai a kaduna.

  Ya kara da cewa ya dace a dauki mataki da wuri domin kada a ci gaba da samun matsalar da ake samu a Jihar Zamfara inda babu zaben fitar da Dan takarar Gwamna a APC Amma kuma Sai ga wata kotu a Jiha ta ce wai an yi zabe, to Muna Kiran a hanzarta daukar mataki domin kada wata Jiha ta dauki irin abin da ke faruwa a Zamfara.

  Shaidanci na faruwa a koda yaushe a cikin jihar zamfara, ana ta kashe mutane a koda yaushe kuma a kowace rana, Amma Gwamna Na faman Yawon Yakin Neman Zabe a ko’ina, saboda haka muke kokarin jan hankalin ayi hattara.

  Wanda irin kalamansa wato Gwamnan Zamfara yake yi tamkar ya saye kowa ne.

  “Ni a matsayina na sanata ban damu ba Ko ban koma kujerar ba Amma dai jama’ar Zamfara sune abin ji sakamakon halin da ake ciki a zamfara a halin yanzu na kashe kashe da wulakanta jama’a dare da rana”. Inji Marafa.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here