Jami’an Tsaro Sun Yi Awon Gaba Da Kakakin Yakin Zaben Jam’iyyar PDP

0
728

Usman Nasidi Daga Kaduna

RAHOTANNI na nuni da cewa jami’an tsaro sun cafke mai magana da yawun kungiyar yakin zaben jam’iyyar PDP na jihar Kaduna a ranar Lahadi, 10 ga watan Fabreru. Wani jami’in jam’iyyar ya tabbatar da cewa, Ben Bako, daraktan watsa labarai da hulda da jama’a na kungiyar yakin zaben jam’iyyar PDP a jihar Kaduna.

An cafke Mista Ben da misalin karfe 11 na safiyar Lahadi a Kaduna.

Rahotannin sun hasko Mista Bako a cikin wani fai-fen bidiyo yana umurtar jama’a da su tayar da rikici idan har aka yi masu ba dai-dai ba a wajen za ben jihar Kaduna.

Sai dai har zuwa yanzu babu wani bayani kan gaskiyar dalilin cafke kakakin yakin zaben jam’iyyar ta PDP, ko kuma cafke shi na da alaka da wannan bidiyo.

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami’an tsaro da ake kyautata zaton cewa jami’an tsaro na farin kaya SSS ne suka cafke Mista Bako tare da wucewa da shi Abuja.

Da ya ke tabbatar da wannan lamari, mataimakin daraktan watsa labarai da hulda da jama’a na yakin zaben PDP, Yakubu Lere, ya ce jami’an hukumar tsaro ta SSS ne suka yi awon gaba da Mista Bako zuwa Abuja.

Ya ce jam’iyyar za ta sanar da matsayarta kan wannan lamari a yammacin Lahadi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here