SAKATARE-Janar na kungiyar ci gaban shiyyar kano ta arewa watau (KANYOPA) Kwamared T. M. Bichi, yace kungiyar zata ci gaba da aiki domin kawo managarcin ci gaba a wannan yanki, musamman a wannan lokaci da take ciki na dimokuradiyya.
Yayi wannan tsokaci ne a hirar su da wakilinmu, tare da jaddada cewa kungiyar ta KANYOPA tana da kyawawan manufofi ga yankin mazabar Dan majalisa ta kano ta arewa, domain a cewarsa, mazabar ta zamo koma baya cikin sauran shiyyoyi dake jihar kano, wanda kuma wajibine a tsaya a yi aikin bunkasa yankin.
Bugu da kari, Kwamared T. M. Bichi ya sanar DA cewa suna aiki DA murya daya kuma a kungiyance, sannan kungiyar tana kokari wajen nemo wasu muhimman aiyuka na alheri daga masu rike madafun iko hukumomin gwamnati domin ganin arewcin kano ta sami ci gaba Mai inganci Lamar kowane yanki.
Sakatare-janar T.M.Bichi ya yi amfani wannan dama wajen jinjinawa sanatan kano ta arewa, Sanata Barau I. Jibrin saboda kokarin take yi wajen Samar ci gaba ta kowane fanni a mazabar sa duk yanayin kasa ke ciki, tareda godewa dukkanin shugabannin kungiyar KANYOPA bisa hada hannu aka yi ana aikin bunkasa kano ta arewa.