Isah Ahmed Daga Jos
WATA baiwar Allah matar aure mai suna Amina Abdulsama da ke zaune a garin Tulu da ke Qaramar Hukumar Toro a Jihar Bauchi ta bayyana cewa tayi shekaru 9, bata ganin mutane sai dai macizai kawai. Amina Abdusalam ta bayyana haka ne a lokacin da take zantawa da wakilinmu.
Ta ce “a kowanne lokaci macizai take gani, bata ganin mutane, kuma yanzu shekaru 9 ke nan tana cikin wannan hali.”
Ta ce farkon faruwar wannan al’amari shi ne wata rana tana zaune da rana, sai taga hoton fuskarta. Daga nan sai wasu mutane suka zo da yawa. Daga nan kuma sai taga macizai sun fito, tun daga nan sai taga bata ganin komai sai macizai.
Acewar ta, shi ne suka tafi asibitin idanu a Bauchi kana bayan sun je asibitin aka duba ta sai suka ce musu su basu ga komai ba.
Amina Abdusalam tayi bayanin cewa sai suka dawo gida suka cigaba da maganin gargajiya, har ya zuwa wannan lokaci.
Itama da take zantawa da wakilinmu mahaifiyar Amina Abdusalam mai suna Mari Halilu ta bayyana cewa wannan al’amari ya faru ne bayan an yi mata aure.
Ta ce tana cikin wannan hali ta haifi ‘yaya mata guda biyu.
‘’Ta ce zata gaya maka dukkan abin da macizan suke yi, wani lokaci su yi ta zagaya ta, wani lokaci har sara suke kawo mata amma kai ba zaka gansu ba, kamar yadda itama ba zata ganka ba’’.
Shima a zantawarsa da wakilinmu yayan Amina Abdusalam mai suna Muhammadu Lawal ya roki jama’a su taimaka masu da addu’a kan halin da wannan baiwar Allah take ciki.
Har ila yau ya roki jama’a su taimakawa wannan baiwar Allah don ta cigaba da neman magani, domin duk wani abun da yake da shi ya kare sakamakon wannan doguwar jinya da suka yi.
To, amma a zantawarsa da wakilinmu wani likitan kwakwalwa da ke a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano Dokta Haruna Yakubu ya bayyana cewa akwai wani ciwo da yake kama kwakwalwa, wanda yake sa mutum ya rika ji ko ganin abin da babu shi.
Ya ce ga bayanin da aka yi, kan wannan abu da yake damun wannan mata, matsala ce ta kwakwalwa. Kuma ga bayanin da aka yi idon wannan mata ya mutu, amma kuma gaskiya ne zaka rika gane ganen abubuwa.
‘’Sau tari idan irin wannan abu ya faru zaka ji mutane suna danganta shi da aljannu da iskoki amma ba gaskiya bane, domin tuni ilmin kimiyya ya riga ya yi bayanin wannan matsala. Ba wasu macizai bane, ta riga ta makance ne amma saboda wannan matsala ta kwakwalwa take wadannan gane gane’’.
Dokta Haruna ya yi bayanin cewa da za a sami mutanen da suka samun irin wannan matsala, zasu dada jaddada wannan bayani.
Ya ce idan aka zo asibiti akwai magungunan da ake baiwa masu irin wannan ciwo, idan suna amfani da su zasu daina wadannan gane gane.
Har’ila yau wakilinmu ya tuntubi Limamin masallacin Juma’a na Unguwar Tudun Wada da ke garin Jos Ustaz Kabiru Muhammed Chidawa don jin ta bakinsa kan wannan al’amari.
Ya ce a musulunci ana iya yiwa mutum sihiri ko kuma mutum ya hadu da Aljannu. Ya ce a cikin suratul Daha Allah ya ce sun tsorata su da sihirinsu sun juye masu idanuwansu da sanduna suka koma ganin sanda a matsayin maciji da igiyoyi.
Ya ce don haka wannan matsala ce ta sihiri kamar yadda Alkura’ani ya nuna. Domin an yiwa Jama’ar Annabi Musa irin wannan sihiri.
Kuma duk manyan malamai sun tabbatar da cewa akwai sihirin da ake yiwa mutum a idanu ya rika ganin wani abu daban, ba ainihin abin ba.
Ustaz Kabiru ya yi bayanin cewa idan irin wannan al’amari ya faru sai mu karanta addu’o’in da Manzon Allah SAW ya karantar damu. Wato mu karanta falaki da nasi da kulhuwallahu sau uku da safe da yamma. Sannan mu yawaita karata surar Fatiha domin Manzon Allah ya ce magani ce. Sannan mu rumgumi karatun Alkura’ani, Allah zai bada dama a warke.