Shugaba Buhari Ya Kasa Daga Hannun Dan Takara A Jihar Zamfara

  0
  686

  Daga Usman Nasidi

  GWAMNAN jihar Zamfara dake a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya kuma shugaban gwamnonin tarayyar Najeriya, Alhaji Abdulaziz Yari da sauran mukarraban sa na jam’iyyar APC sun sha kunya bayan da shugaba Buhari ya ki daga hannun dan takarar gwamna a jihar.

  Mun samu cewa dai rikicin ‘yan takarar jam’iyyar APC a jihar ta Zamfara ne dai ya hana shugaba Muhammadu Buhari daga hannun dan takarar gwamna a jihar.

  A yayin yakin neman zabensa a Zamfara a ranar Lahadi, Buhari ya ce “duk gardamar da ake idan abu yana wurin shari’a za mu dakata.”

  Hakan dai ya kara tabbatar da cewa APC a Zamfara na cike da rudani bayan shugaban ya kasa daga hannun ‘yan takara.

  Kafin jawabin Buhari, gwamnan jihar mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya ce ba za su tilasta wa shugaban daga hannun ‘yan takara ba kamar sauran jihohi amma ya ce da yardar Allah da ‘yan takarar APC za a yi zaben 2019.

  A cikin jawabinsa a Zamfara, shugaba Buhari ya ce yana fatan kafin ranar Asabar, hukumar zabe za ta fito ta fadi dan takarar da ta yadda da shi.

  Sai dai kuma Buhari ya yi kira ga mutane su fito su zabi wanda suke so, a gaban gwamnan Zamfara da ke gawagwarmayar tabbatar da kwamishinansa na kudi a matsayin gwamna.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here