Rundunar ‘Yan Sanda Ta Haramtawa Jami’anta Rike Bindiga A Rumfunan Zabe

0
756

Daga Usman Nasidi

MUKADDASHI shugaban ‘yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, ya ce sun haramta wa jami’ansu zuwa rumfar zabe dauke da bindiga, babban sufeton ya bayyana haka ne ranar Laraba, 13 ga watan Fabrairu a daidai lokacin da zaben Shugaban kasa da nay an majalisar dokoki ya rage kwanaki uku kacal.

Adamu ya bayyana hakan ne a lokacin da tawagar tarayyar turai da ta zo sanya idanu akan zabukkan kasar ta kai masa ziyara a hedkwatar rundunar da ke Abuja.

Ya kuma kara jadadda musu cewa jami’ansu zasu yi aiki sanya idanu da kuma bada tsaro a rumfunan zaben.

Sufeton ya bayyana cewa jami’ansu zasu tabbatar da dokar nan ta takaita zirga-zirga ta yi aiki kamar yadda dokokin zabe suka tanada, sannan rundunar zata hada kai da sauran jami’an tsaro wajen tabbatar da tsaro tun daga fara zaben har zuwa lokacin da za a bayyana sakamakon zaben, dama bayan zaben.

Idan ba a manta ba, rundunar yan sanda ta gargadi yan siyasa da su guji siyan kuri’u a ranar zabe ko kuma su fuskanci doka.

Mataimakin sufeto janar na yan sanda da ke kula da hedkwatar rundunar, Abuja, Usman Tilli, ya yi gargadi a Gombe a ranar Talata , 12 ga watan Janairu yayinda yake jawabi da masu ruwa da tsaki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here