Soja 1 Da Mutane 2 Sun Rasa Rayukan Su A Harin Tawagar Gwamnan Borno

0
673

Daga Usman Nasidi

WANI Jami’in soja daya da masu farar hula biyu sun rasa rayukansu a ranar Laraba yayin da yan Boko Haram suka budewa gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, wuta a yankin Borno ta Arewa yayinda yaje yakin neman zabe.

Wata majiya mai karfi ta tabbatar da hakan ga jaridar The Nation. Ya ce an yan ta’addan sun kai farmakin ne a Gajibo, karamar hukuma Dikwa na jihar Borno.

Majiyar ta bayyana cewa Shettima ya tsira ba tare da wani rauni ba saboda harin ya shafi motocin da ke bayansa ne.

Yace: “Abin takaici ne yan Boko Haram sun yi amfani da daman tsawon motocin gwamnan. Lokacin da abinda ya faru, gwamnan ya riga ya wuce.”

“Mutane uku sun rasa rayukansu- soja daya da masu farar huka biyu.

Yanzu muke dawowa daga Maiduguri.”

Ku saurari cikakken rahoton…

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here