Yaki Da Maleriy: Kungiyar (WHO) Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Mata Da Yara 854,000 A Borno

0
1126

SANI GAZAS CHINADE DAGA DAMATURU

A KOKARIN ta na rage yaduwar cutar zazzabin cizon sauro (maleria) a jihar Borno, kungiyar lafiya ta duniya, (WHO) ta tsara raba wa mata masu ciki hadi da kananan yara kimanin 854,000 magungunan kashe cutar a jihar.

Kaddamar da raba magungunan a karkashin kulawar wani kakkarfan kwamitin sa-kai da zai bi gida-gida za a raba su ne a kananan hukumomi bakwai (7) a jihar.

An gudanar da raba magungunan yaki da cutar maleriya na kwanaki hudu, a birnin Maidugurin, yadda babban jami’in WHO, na kasa da ke kula da arewa maso-gabas, Dokta Iniabasi Nglass ya ce wadannan nau’i na magungunan yaki da cutar maleriya domin yara ‘yan shekara uku zuwa biyar ne.

Babban jami’in ya kara da cewa “mun tsara a cikin wannan shekara ta 2019- wajen yaki da cutar maleriya ga kananan yara kimanin 854,000, hadi da mata masu ciki, a kananan hukumomi bakwai (7) da suka kunshi Maiduguri, Jere, Mafa, Kala/Balge, Guzamala, Damboa da Mobbar”.

“kuma hanya daya daga cikin hana yaduwar cutar maleriya a tsakanin mata masu ciki, shi ne- baya ga raba gidajen sauro, sai kuma magungunan yaki da cutar ga mata masu cikin, a kan kari kuma lokaci bayan lokaci, tare da ziyartar cibiyoyin kiwon lafiya”.

Bugu da kari kuma, Dakta Ngalass, ya ce “sannan kuma wannan ita ce kadai hanya, wanda babu wani siddabaru a yaki da cutar maleriya da ya wuce kawar da ita a cikin wadannan yankuna da ta shafa”.

Ya kara nuna cewar, “dole a rika amfani da gidajen sauron da aka saka wa magani. Domin kaucewa cizon sauron, wanda yake yada cutar ga mata masu ciki zuwa jirajiran da ake haifa”.

A cewarsa  dole a kowanne lokaci a rinka tsaftace muhallan da cutar maleriya ta shafa, tare da gusar da duk wani malaba wadda sauron zai makale tare da kawar da kwantaccen ruwa dake kewaye da gidajen mu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here