Zaben 2019: Muna Maraba Da Kowa A Akwa Ibom – Udom 

  0
  949
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
  A KOKARIN ganin an yi zabe cikin kwanciyar hankali da Lumana, Gwamnatin Jihar Akwa Ibom karkashin jagorancin Gwamna Udom Emmanuel ya yi Karin jan hankalin ga daukacin al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu kuma su yi zabe cikin natsuwa da lumana domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan su na tsayawa zabe Ko kuma a zabe su.
  Zaben da za a yi na shugaban kasa da yan majalisun tarayya da na Dattawa Gobe muka Kiran jama’a da su yi zabe cikin tsari ba tare da magumagu ba.
  A cikin wani jawabin da Gwamnan Jihar Akwa Ibom ya karanta wa mutane Jihar inda yake Kiran jama’arsa baki daya cewa hakika yan takarar nan sun bayyana maku munufofinsu suna kuma yin kira a gareku domin taimaka masu Ku ba su damar darewa kan madafun iko.
  Bayanin Gwamnan ya ci gaba da cewa kamar yadda kowa ya sani cewa Jihar mu wuri ne da ke da zaman lafiya da zaman tare cikin lumana. Don haka a kokarin Ku na yin zabe cikin kwanciyar hankali domin sauke nauyin da ke kanku, Ina kiranku da ku ci gaba da riko sunan da jihar Akwa Ibom ke da shi na zaman lafiya a kowane lokaci.
  Mu dukkan mu yan uwan juna ne don haka kada Ku amincewa duk wani Ko wasu gungun jama’a da za su kokarin salwantar rayuwar Dan Jiha Ko wanda ya kawo ziyara a Jihar.
  Ina kara jan hankulanku da kada Ku mance da abin da Littafin baibul ya fada a cikin aya ta daya sura ta Goma a game da yan uwantaka da tsarin zaman tare cikin kwanciyar hankali da lumana.
   Don haka yaku yan uwana, kada Ku sake ku Saka kanku  cikin duk wani al’amarin da zai kawo tabarbarewar tsarin doka da Oda.
  Ga irin abin da tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton ya ce ” zamu iya yin abubuwa masu kyau ne idan mun yi aiki tare. Bambance bambancen mu na nan Amma kuma kasancewar mu al’umma daya shi ne babban Abu”.
  Koda yake Muna da Jam’iyyun siyasa daban daban, a Jihar Akwa Ibom, Amma abin da ya hada mu a matsayin yan uwana juna ya Fi na wanda yake na Wuccin gadi da zai zo ya wuce, ya kuma bar mu tare.
  Ga shugabannin mu kuwa Bari in yi amfani da maganar wani shugaban Amurka, John Quincy Adam da ya ce ” idan abin da kake yi zai iya sanya wadansu su yi mafarki kuma su kada fadaka, su yi aiki su kuma zama wasu cikin al’umma, lallai Kai shugaba ne domin kayi abin da ya amfani sauran mutane”. Saboda haka Muna fatar ayyukan shugabannin mu za su taimaka mana ta fuskar ci gaba mu zama wani Abu a rayuwa da kuma kiyaye doka da Oda musamman ganin cewa makamar yayan mu da jikoki da dukkan na baya da mu ta dogara ne a wuyanmu ta ayyukan da muke yi.
  Ina yin maraba lale ga dukkan baki da masu sanya idanu ga harkokin zabe da suka ziyarci Jihar mu domin su tabbatar da harkokin Dimokuradiyya Muna son tabbatar maku cewa tsaron lafiya da dukiyar Ku babu wata tantama a kan hakan, don haka Muna maraba da kowa da kowa cikin mutunci da salama za a yi zabe lafiya a Gama lafiya.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here