Atiku Ya Kwancewa Buhari, APC da INEC Zani A Kasuwa, Ya Ja Hankalin ‘Yan Nageriya

0
872

Daga Usman Nasidi

TSOHON mataimakin shugaban kasa kuma Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya bukaci ‘yan Nigeria da su kasance masu daukar hakuri akan wannan mataki da hukumar zabe mai zaman kanta ya kasa INEC ta dauka na dage zaben shugaban kasar.

Atiku ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya sawa hannu da kansa a safiyar ranar Asabar, a matsayin martani kan matakin da INEC ta dauka na dage babban zaben kasar kamar yadda shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya sanar.

Atiku ya sa hannu akan sanarwar a matsayin jawabi kai tsaye ga ‘yan Nigeria, daga Yola, jihar Adamawa inda ya koma domin kad’a kuri’arsa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce abun takaici ne ace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta gaza yin amfani da dogon lokacin da ta samu wajen shiryawa zaben.

Ya ta’allaka wannan mataki na INEC da karin maganar nan ta “Biri da shan duka, gardi da karbar kudi. ”

Atiku ya shawarci ‘yan Nigeria da su rungumi zaman lafiya tare da danne zuciyarsu akan yin fushi da wannan mataki, yana mai cewa “Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana ha maza ha mata sai ya yi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here