APC Za Ta Yi Magudi Cikin Yankuna 3 Na Najeriya A Babban Zabe – Atiku

  0
  870

  Daga Usman Nasidi

  DAN takarar kujerar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi zargi da cewar jam’iyya mai ci ta APC ta daura duk wata damara ta tafka magudi a yayin babban zaben kasa domin rinjayar da nasara a kanta.

  Atiku wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya ya bayyana cewa, jam’iyya mai ci ta APC ta daura damarar tafka magudi a yayin babban zaben kasa ta hanyar ribatar na’urarar tantance masu kada kuri’a wajen kulla dabaru na ha’inci.

  Dan takarar ya yi ikirarin hakan ne a ranar Talata yayin taron jiga-jigan jam’iyyar sa ta PDP da aka gudanar a hedikwatar ta da ke babban birnin kasar nan na tarayya.

  Atiku ya yi ikirarin cewa, tuni jam’iyya mai ci ta APC ta mallaki wasu na’urorin zamani na daban domin gaggauta gudanar da zabe cikin wasu yankunan kasar nan da ta ke hasashen samun nasara yayin da za ta kawo jinkiri gami da haifar da nawa a yankunan da ba za ta yi nasara ba.

  Wazirin Adamawa ya yi zargin cewa, jam’iyyar APC ta horas da wasu kwararrun ma’aikata a kasar Sin da tuni su ka dawowa kasar nan ta Najeriya domin ribatar kwazon su wajen tabbatar da cikar burin ta yayin babban zaben kasa.

  Cikin jerin yankunan kasar nan da jam’iyyar APC za ta kawo jinkiri tare da haifar da nawa yayin gudanar zabe kamar yadda Atiku ya wassafa sun hadar da; Kudu maso Kudu, Kudu maso Gabas da kuma Arewa ta Tsakiya.

  Sauran yankunan uku da jam’iyyar APC za ta gaggauta gudanar zaben domin samun yalwa ta fuskar yawan adadi na masu kada kuri’u sun hadar da yankin Arewa ta Gabas, Arewa da Yamma da kuma Kudu maso Yamma.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here