AN bayyana cewa dage zaben shugaban kasa da aka yi ba zai hana kungiyar BCO bayyana sahihancin Shugaba Muhammadu Buhari ba, musàmman ganin yadda take gudanar da jagorancin al’uma cikin nasara.
Wannan bayani ya fito ne daga mataimakiyar shugabar Kungiyar mai kula da arewacin kasarnan, Hajiya Halima Ben Umar yayin ganawar su da wakilinmu dangane da dage zaben shugaban kasa da akayi na kwanaki bakwai.
Tace Kasarnan tana bukatar samun ci gaba, da zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki da sauran abubuwa muhimmai domim ganin kowane dan kasa yana rabautà daga aikace-aikace na alheri kamar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari keyi yanzu.
Dangane da dage zaben da hukumar zabe ta kasa tayi, ya faru ne bisa wasu dalilai da hukumar zaben take dasu wadanda kuma dole suka sanya aka dage zaben har sai ranar 23 ga wannan wata kamar yadda kowane dan kasa ya gani.
A karahe, Halima Ben Umar tayi amfani da wannan dama wajen sake yin kira ga masu zabe dasu zabi Buhari a matsayin shugaban kasa ta yadda za’a sami ingantaccen ci gaba ta kowani fanni.