Ana Bin Tsauraran Matakai Na Tantance Fim Kafin Aba Mutum Kyauta — Yusuf Magarya

0
1644
Musa Muhammad  Kutama Daga kalaba
KWANAN baya kungiyar Matasan Arewa ta Najeriya ta karrama fitaccen mai shirin fina-finan Hausan kamfanin Magarya fim production dake Kanon Dabo wato Yusuf Muhammad Magarya . Wakilin mu a kalaba musa Muhammad kutama ya yi kacibis da jarumin na shirya fina-finan Hausa a kalaba inda suka tattauna akan matsalar yadda rashin iya rubuta labarin fim kan gimshi mai kallo da kuma karramawar da kungiyar matasan Arewa a Najeriya ta bashi lambar yabo.
Ga yadda tattaunawar su ta kasance:-
GTK: Akwai wasu daga cikin masu kallon fina-finan hausa na ganin ana samun kasawa a wasu fina-finan ku yadda yake gundurar mai kallo baya iya tsayawa yaci gaba da kallon sa har karshe, mai kake jin ke haifar da haka, sannan ku masu kamfanonin shirya fim  kuna sane kuwa da waccan matsala?
Yusuf Magarya : farko sunana Yusuf Muhammad Magarya, mai shirya fim na kamfanin shirya fina-finai na  Magarya Production dake jihar kano.
Eh! bazan ce maka ba’a samun irin waccan matsala ba, matsalar akwai ta amma ba’a kowanne fim ba yawanci dai duk fim din da
mai kallo zai kasa kallo guda daya, har ace ya cire bai masa dadi ba ya kasa ci gaba da kallon sa duk dan Adam ajizi ne, tara yake bai cika goma ba.
Akwai wannan wani lokaci duk yadda kayi da kokarinka sai an samu wani wurin da mutum ajizanci ya dan taba shi, sannan abu na biyu shi ne duk fim din da kasa kaga labarin bai yi maka ba, ka tsaya ka duba kaga na wane kamfani ne yayi fim din kasan fa akwai masu yin fim akwai kuma muna fim yanzu ace ka kalli fina-finan kamfanin UK Entertainment, ko na Mai shadda Investment, ko FKD da irin su Sheshe Movies ko ka kalli na Magarya productions, ai kasan fina-finan su sun
tsere tsara na tabbata idan ka kalli fina-finan kamfanonin da na zaiyana maka na tabbata bazaka kalli fina-fina su kaji cewa sun ginshe ka ka cire nasan ba zaka iya kyalewa scene 1 ko 2 ya wuce ka ba, sai ka
kalla har karshe ko kace bai yi maka dadi ba.
Kasan ako wace harka akwai ‘yan koyo to ta iya yiwuwa idan Allah ya hada ka da na ‘yan koyo aka yi dace sabon producer ne ko sabon darakta ne, yana kokari ya koyi sana’a ne aka zo aka fara nuna fim din sa da ya yi, to a irin wadan can fina-finai ne za a iya samun irin wadancan matsaloli idan ka hau da irin fina-finan wadancan kamfanoni, to dole kaji abu ya ginshe ka sannan ma da wane ne ya rubuta labarin, idan ka hadu da irin wadancan kamfanoni dole kaji fim din ma ya fice maka daga rai
ka cire  shi.
GTK:- Kamfanonin dake shirya fina-finan hausa a kannywood da kuma wadanda suka yi fice wajen kwalliya da kuma samar da wurin wasa na samu kyauta daga kungiyoyi daba na gwamnati ba Najeriya da wajen ta, wadan ne hanyoyi ne ake bi harma aba mutum kyauta?
Yusuf Magarya: Ah! Batun bayar da kyautuka da ake kira da Award, akwai
hanyoyi da yawa da ake bi ake dubuwa. Na farko duk wani wanda ka gani an bashi kyauta wato Award, to gaskiya sai an zauna an duba fim din sa kuma sai ya cike takardar son neman ya samu kyauta daga cikin wadanda za a tantance tunda akwai kamfanoni, jarumai da dai sauran hanyoyi da ake bi ake dubawa kafin a tantace aba wanda ya yi nasarar kyautar.
GTK: Ta yaya ake tantancewar musamman kamfani ko jarumi dama wani wanda ya yi fice a wani bangare na fim aba shi kyauta?
Yusuf Magarya: Alhamdulillah, mun godewa Allah kwanan baya kamar wata daya haka da ya wuce na samu kyauta Award. Wani za kaga anbi mataki ta
bangaren wanda ya fi kowa iya yiwa ‘yan wasa kwalliya, wani kuma bangaren darakta wasu kuam ta bangaren jarumi mai tasowa ko kuma wanda yafi kwarewa a iya siddabaru wato effect na cikakken jarumi ko jaruma, wani lokaci anabin kamfanin da yafi kowa ne iya shirya fim su masu tantancewa sune zasu tsaya su kalla suga wanda yafi abashi kyauta.
GTK: kana daya daga cikin wadanda kungiyar matasan Arewa taba kyautar
kamfanin da ya yi fice, bamu labarin yadda aka zabo ka cikin ‘yan takarar gasa har ka yi nasara?
Yusuf Magarya: Alhamdulillah mun godewa Allah kwanan baya kungiyar
matasan Arewa ta bani kyauta wato Award wata kungiya ce ta samarin Najeriya wadda ake kira da Arewa Kutashi Award, kungiyace wadda take shirya kyaututtuka irin wadannan domin zaburar da samari su rike sana’a ba tare da sun dogara da aikin gwamnati ba, to wannan kungiya ta
karramani a matsayin ni ne wanda kamfani na ya fi ko wane kamfani a wannan
shekara 2019 iya shirya fim, amma hakan ba yana nufin ni na fi sauran bane ko kuma su basu iya ba ne, don ni nq shiga takarar ne da wani fim mai suna “Madubin Dubarudu”.
GTK : Ta ya ya aka tantance ka har ka  samu kyauta?
Yusuf Magarya: Alhamdulillahi yadda aka tantance ni su masu shirya wannan gasa sukan dauki fina-finai kamar kwara uku zuwa hudu kuma kamar mutum goma ko fiye da haka zasu baje fim din ka, yayin damasu duba yadda ka dauki fim daban, masu duba yadda kasa fitila ma daban, wanda ke duba murya ma daban, wadancan mutane idan sun zauna sun tantance sune suke bada abinda ya fi a kowane daga cikin fina-finan da suka tantance to wannan fim dana gaya maka madubin duba rudu shi ne aka zaba matsayin wanda ya fi aka bani kyauta.
GTK: Wane tanadi ake yi wa rayuwa ganin cewa wasu da suka jima suna harkar fim kan kare basu da mahalli ko kuma wani jari da zasu rike rayuwar su?
Yusuf Magarya: Tanadi dai insha Allahu bai wuce daya ko biyu ba, wato gaskiya da rukon amana. Kaga duk wanda yake rike da jari yana kuma taimakawa ’yan uwa babu laifi.
GTK: Wane sako kake dauke da shi ga masu bibiyar fina-finan kamfanin ka?
Yusuf Magarya: Sakona gare su na farko ita ce ina alfahari dasu kuma lambobin
da muka sanya a jikin fastar fim ko a jikin sa muna bayarwa ne domin inda aka ga gyara a kira mu ayi mana bayani zamu gyara don koda yaushe kofa bude take na karbar gyara da shawarwarin ku tunda dama domin bukatar ku ce mu keyin harkar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here