Zargin Da Dogara Ya Yi Wa Gwamnan Bauchi Kan Ma’aikatan Bogi Soki Burutsu Ne – Kungiyar Matasa

0
1128

Isah Ahmed Daga Jos

KUNGIYAR wayar da kan matasa da al’ummar Jihar Bauchi kan manufofin gwamnan Jihar M A Abubakar [GMAACA] ta bayyana cewa, zargin da Kakakin Majalisar Wakilai ta tarayya Yakubu Dogara ya yiwa gwamna M A Abubakar cewa wai yana samun naira biliyan 4, a duk wata ta hanyar ma’aikatan bogi da ake da su a jihar soki burutsu ne. Kungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa mai dauke da sanya hanun Kakakin kungiyar Nura Mohammed  da ta rabawa ‘yan jarida a garin Bauchi,

Kungiyar ta ce wannan zargi soki burutsu ne,  kuma an yi shi ne saboda ganin lokacin zabe ya zo don haka kungiyar ta yi kira ga al’ummar Jihar Bauchi,  su yi watsi da wannan zargi mara tushe.

Ta ce  “tun da aka dawo mulkin damakoradiya a Najeriya, ba a taba samun gwamnan da ya ke da manufofi na kyautatawa al’ummar Jihar ba, kamar gwamna M A Abubakar ba.

Ta kara da cewa gwamna M A Abubakar  mutum ne mai akida mai kishi  da yasa al’ummar Jihar Bauchi a gaba, domin ganin sun sami cigaba.

Acewarta, gwamna M A Abubakar ya yi abubuwa da dama na kyautatawa al’ummar Jihar Bauchi. Gwamnan  ya kirkiro hanyoyi da dama da matasan Jihar Bauchi suka sami abin dogaro da kawunansu. Ya gina sababban asibitoci a dukkan kananan hukumomin Jihar Bauchi guda 20, tare da samar da magunguna. Ya bunkasa ilmi a Jihar ta hanyar gina makarantu da samar  da kayayyakin aiki,  kuma ya gina hanyoyi. Don haka a matsayinmu na matasa masu kishin Jihar Bauchi, muke goyan bayan  ya cigaba.

Kungiyar ta ce ya zama wajibi ga dukkan mai kishi Jihar Bauchi ya sake zabar Gwamna M A Abubakar  a karo na biyu. Domin ya cigaba da waxannan ayyuka da ya sanya a gaba.

Hakazalika ta bayyana cewa babban aikin da suka sanya a gaba shi ne wayar da kan al’ummar Jihar Bauchi kan ayyukan da gwamna M A Abubakar ya yi a Jihar Bauchi.

Ta ce ‘’Yanzu  muna da mambobi a dukkan  lunguna da kauyuka na  dukkan kananan  Jihar Bauchi,  da suka tashi tsaye dare da rana wajen gudanar da wannan aiki, na wayar da kan al’ummar Jihar Bauchi kan ayyukan gwamna M A Abubakar’’.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here