An Harbe Mutane 4 A Jihar Ribas

0
800

WASU yan baranda sun bindige mutane hudu, biyu manyan jigogin jam’iyyar All Progressives Congress APC a karamar hukumar Andoni ta jihar Ribas, yankin Neja Delta.

Kakakin hukumar yan sanda na jihar Ribas Omoni Nnamdi, ya tabbatar da hakan ne bayan jam’iyyar APC ta kai kuka.

Kakakin jam’iyyar APC na jihar yace: “Yan barandan PDP sun bindige jigogin jam’iyyar APC a Asarama, Cif Mowan Etete.”

Banda shi, an kashe babban yayansa da kuma wani dan’uwansa a jihar. Na hudun kuma, wani mutumi ne mai suna Ignatius, dan jam’iyyar APC. Ya rasa rayuwarsa a Ajakaka, Adoni.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Mista Nnamdi ya tabbatar dalabarin inda yace: “Hakane, muna da labari. Muna kokarin damke wadanda sukayi kisa kuuma munyi kokarin kwantar da kuran.”

Gabanin zabe, Mista Nnamdi ya bayyanawa manema labarai cewa hukumar yan sanda zasu tabbatar da zaman lafiya a jihar Ribas.

An fara harbe-harbe a a PU 14, Ward 8, karamar hukumar Ubima ta jihar RIbas.
Ubima itace mahaifar ministan sufuri kuma dirakta janar da zaben shugaba Buhari, Rotimi Chibuike Amaechi.

Wata jami’ar hukumar FRSC ta kai kuka ga abokan aikin ta hanyar kiransu a wayar tarho domin su kawo dauki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here