Zaben 2019: Yadda Al’amura Ke Wakana A Bangarori Daban Daban Na Kasar Nan

  0
  960

  Daga Wakilenmu Na Jihohi

  A SAFIYAR yau asabar ne aka fara gudanar da zabubbuka wanda ya hada dana Shugaban Kasa, Sanatoci da Yan Majalisar wakilai na tarayyar kasar Najeriya.

  Kamar yadda rahotanni suka bayyana daga wajen wakilen mu dake wasu garuruwa da shiyoyi daban-daban na kasar, sun bayyana cewa al’umma da dama sun yi turuwa zuwa wajen kada kuri’ar.

  Rahoton da muka samu daga garin katsina ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC da iyalen sa, na daya daga cikin wadanda suka fara kada kuri’ar su a garin Daura, to amma Izuwa yanzu ba mu samu labarin dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP Atiku Abubakar ko ya kada na shi kuri’ar ba.

  Hakazalika tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Muhammadu Namadi Sambo tare da uwargidansa Hajiya Anima Namadi Sambo sun bayyana gamsuwa da irin yadda mutane suka samu fitowa domin kada kuri’unsu domin zaben shugaban kasa da kuma mataimakinsa.

  Sun dai kada kuri’ar ta su ne a mazabar kwalejin yan sanda da ke cikin garin  kaduna.

  Rahotanni daga jihar Adamawa na bayyana cewa Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya gaza kawo rumfar mazabarsa a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya lallasa shi.

  Atiku ya samu kuri’u 167 ya yinda Buhari ya samu kuri’u 186 a rumfar zabe mai lamba 012 da ke gundumar Ajiya, a Yola, inda Atiku yayi zabe.

  Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC ya doke babban abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a akwatin zaben tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun a zaben yau Asabar 23 ga watan Fabrairu.

  Yayin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu kuri’u 87 a zaben shugaban kasar, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta samu kuri’u 18 ne kacal.

  Dukda yake akwai matsaloli na rashin kawo akwatinan zaben da wuri, a yayin da wasu guraren ba a fara zaben da wuri ba, hakazalika wasu mazaben basu san halin da suke ciki ba wanda rahotanni ya alakanta lamarin da laifin Hukumar zabe.

  Wasu jama’a dake mazabu daban-daban a garin Kaduna na ta korefe-korafe dan gane da irin matsalolin da ake fuskanta musamman na na’urar tantance mutanen da ake ta samun tsaiko ta kan shi saboda kin yin aikin da yake ko kuma tsayawa a yayin da ake cikin aikin.

  Hakazalika daga garin Kano, wakikin mu ya bayyana cewa masu zabe suna kan layi tun safe domin ganin sun jefa kuri’ar su a rumfar zaben su kamar ta Unguwar Fa Dungurawa dake Mazabar Gargari cikin yankin karamar hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.

  Izuwa yanzu da muka kawo muku wannan labarin, al’amura na tafiya daidai yadda ya kamata ba tare da wani tashin tashina ba a wurare da dama.

  Sai ku ci gaba da bibiyar don karin bayanai kan yadda al’amura ke gudana.

  Ga kuma hotunan yadda al’amura ke gudana a wasu sassa na kasar

  Babban Sakataren Jam’iyyar APC kuma dan takarar kujerar gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mai Mala Buni, ya bayyana matukar gamsuwar sa dangane da yadda jama’a suka yiwa rumfunan zabe cikar kwari, ranar zaben shugaban kasa tare da na ‘yan majalisun tarayya guda biyu.

  Alhaji Mai Mala Buni ya bayyana hakan ne a ganawarsa da manema labarai jim kadan da kada kuri’ar sa a mazabar sa da ke phase one, a babban birnin jihar Yobe garin Damaturu.

  Babban sakataren dai ya isa rumfar zaben da kimanin karfe11:30; na safe a cikin cincirindon jama’a, wanda nan take jami’an zaben suka tantance shi tare da jefa kuri’ar sa.

  Kammala kada kuri’arsa ke da wuya, sai dan takarar ya bayyana gamsuwar sa dangane da yadda mutane suka yi dandazo domin jefa kuri’arsu.

  Daga nan sai ya yi kyakkyawar fata ga dukannin al’ummar jihar kan a gama zabe lafiya ba tare da saba ka’idar hukumar zabe ba don kaucewa shiga halin hawula’i.

  Dan takarar gwamnan, ya shaidar da cewar, ya gamsu da goyon bayan da jama’ar jihar Yobe ke ci gaba da baiwa jam’iyyarsu ta APC, tare da kara bayyana cewa,
  “bisa ga wannan ne ya sa muke da kwarin gwiwar lashe wadannan zabukan cikin yardar Allah SWT”.

  Ya kara da cewar, “muna kara kira ga jama’ar jihar Yobe da cewa, su sake fitowa kwan su da kwarkwatarsu, a zaben gwamnonin dake tafe don kara jefa kuri’arsu ga jam’iyyarsu ta APC”.

  A yayin da aka kammala kad’a kuri’u a wasu sassa na jihohi 36 na kasar Nigeria, ciki kuwa har da jihohin Sokoto, Jigawa da Kebbi, tuni aka fara tattara kuri’u tare da kidaya su a wasu rumfunan zabe na jihohin.

  Sai dai har zuwa yanzu akwai rumfunan zaben da ba su kammala kad’a kuri’arsu ba.
  HATTARA: Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ce kadai ke da ikon tattara kuri’u da fadin sakamakon zabe.

  Bayanai a kan sakamakon kuri’un da aka kada a mazabun da zaka karanta a wannan shafin ba daga hukumar INEC ya ke ba. Legit.ng Hausa ba za ta iya tantance gaskiyar sakamakon ba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here