An Sako Mutane 18 Masu Yi Wa Kasa Hidima Da Aka Sace A Akwa Ibom

0
830

Musa Muhammad kutama daga kalaba

AKALLA masu yiwa kasa hidima goma sha takwas da suke yiwa hukumar zabe mai zaman kanta aikin zabe aka sace a wurare daba-dana na jihar Akwa Ibom ranar Asabar lokacin da suke bakin aikin na yin zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisar wakilai dana tarayya.

Shugaban hukumar zabe a jihar Akwa Ibom Mike Igini ne ya sanar da haka ga manema labarai a garin Uyo wanda ake zargin ‘yan bindiga ne don neman fansa.

Shugaban hukumar ya bayyana cewar a wurare daban-daban na kananan
hukumomin Abak, da Ikot Ekpene mazabar tsohon gwamnan jihar, sanata Godswill Akpabuyo aka kama mutune goma daga cikin su.

Acewarsa, an dauke hudu ne a karamar hukumar Ikono yayin da aka kama sauran hudun a Itu karamar hukumar Itu.

Ya ci gaba da cewa jin haka keda wuya ya sanarwa kwamishinan ‘yan sandan jihar halin da ake ciki inda nan take ya baza jami’an sa suka shiga nema su kafin a tashi zabe inda aka sako mutum goma daga cikin su ayayin da ragowar hudun suma daga baya aka sako su.

Dangane da kudin fansa kuwa, shugaban hukumar zaben jihar baiyi wani Karin haske ba na ko sun bada kudin fansa ko basu bada ba kafin masu garkuwa da mutanen su sako su.

Wakilin mu da ya tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Odiko MacDon domin jin tabakin rundunar game da garkuwa da masu yiwa kasar hidima sai ya ce “labarin bai kaiga iso mana ba amma na yi magana da daraktan hukumar masu yiwa kasa hidima a jihar yace bashi da masaniya ko har hakan ta faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here