INEC Ta Dage Sanar Da Sakamakon Zaben Shugaban Kasa Zuwa Litinin

0
1023

Daga Usman Nasidi

HUKUMAR zabe mai zaman kan ta (INEC) ta sanar da daga sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka kamala a jiya, Asabar, da yau, Lahadi, a wasu mazabun.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da aka nuna kai tsaye yayin da ya ke sanar da bude cibiyar tattara sakamakon zabe ta kasa da ke Abuja.

Ya bayyana cewar za a fara sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da misalign karfe 11:00 na safe.

Fafesa Yakubu ya ce kwamishinonin zabe (REC) daga jihohi 36 da birnin tarayya za su gabatar da sakamakon zabe na jihohin su.

Yanzu haka kallo ya koma cibiyoyin tattara sakamakon zabe da ke fadin kasar nan, inda ake cigaba da samun labarai daga wakilan jam’iyyu da kuma turawan zabe.

An samu labarin tashin hankali da rigingimu a wasu cibiyoyin, a wasu cibiyoyin ‘yan dabar siyasa sun kai hari yayin da a wasu wuraren aka rawaito cewar jami’an tsaro na korar ma su sa-ido da manema labarai.

A ranar asabar ne miliyoyin ‘yan Najeriya su ka fita domin zaben shugaban kasa da zai shugabanci Njeriya a cikin shekaru hudu ma su zuwa.

Kazalika sun zabi ‘yan majalisar tarayya da za su wakilce su na tsawon shekaru hudu a majalisar tarayya.

Akwai kujeru 468 a majalisar tarayya ta kasa: 109 a majalisar dattijai da kuma 360 a majalisar wakilai.

Akwai ‘yan takarar kujerar shugaban kasa 73 amma takarar ta fi daukan hankali tsakanin shugaba Buhari na jam’iyyar APC da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here