Saraki Ya Sha Kaye A Dukkanin Kananan Hukumomi 4 Na Yankin Sa

  0
  808

  Daga Usman Nasidi

  SHUGABAN majalisar dattawa, Bukola Saraki ya fadi a dukkanin kananan hukumomin da ke yankinsa na Kwara ta tsakiya a zaben da aka gudanar a ranar Asabar.

  Kananan hukumomin sune Asa, Ilorin South da kuma Ilorin East. Na hudun shine Ilorin West, wanda ya kasance ainahin karamar hukumar Shugaban majalisar dattawan.

  Sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta ta fitar ya nuna cewa APC ta samu 51, 531 yayinda PDP ta samu 30,075.

  Yawan masu rijista ya kasance 224, 494, yayinda wadanda aka tantance ya kama 91,130.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here