Yan Adawa Ba Za Su Sami Nasara Ba Kan Zaben Gwamnan Jihar Bauchi Ba – Abdullahi Zabala

  0
  994

  Isah Ahmed Daga Jos

  WANI dan siyasa a Jihar Bauchi Alhaji Abdullahi Sale Bare [ Abdullahi Zabala] ya bayyana cewa duk da cewa wasu  jam’iyyun adawa a Jihar,  sun sami wasu kujerun ‘yan majalisun tarayya a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a Jihar. Hakan ba zai taba yin tasiri ba, kan sake zaben gwamnan Jihar M A Abubakar a zaben gwamnan jihar  da za a gudanar, a ranar asabar mai zuwa. Alhaji Abdullahi Zabala ya bayyana haka ne,  a lokacin da yake zantawa da wakilinmu.

  Ya ce gaskiya samun nasarar wasu kujerun  ‘yan majalin tarayya  da jam’iyyun adawa suka yi a Jihar Bauchi, babu wata matsala da zai kawo wajen samun nasarar sake zaben gwamnan Jihar Bauchi M A Abubakar, a zaben gwamnan jihar da za a gudanar.

  Ya ce domin idan aka dubi yawan kuru;un da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a Jihar, kusan dubu 800 ya nuna cewa jam’iyyun adawa basu sami wata nasara ba a Jihar.

  Ya ce don haka muna da kyakyawan zaton cewa  al’ummar Jihar Bauchi zasu fito su zabi gwamna M A Abubakar da yawan kuru’un da suka  fi na shugaban kasa,  a wannan zabe da za a gudanar.

  Alhaji Abdullahi Zabala ya yi bayanin cewa abin da yasa jam’iyyum adawa ba zasu sami nasara kan gwamna M A Abubakar ba, a zaben gwamnan da za a gudanar.   Shi ne saboda irin ayyukan alherin da ya yi a Jihar.

  ‘’Gwamna M A Abubakar ya gina sababbin asibitoci a kananan hukumomi 19 a cikin kananan hukumomi guda 20 da ake da su. Haka kuma ya bunkasa harkokin ilmi a Jihar, tare da  ayyukan hanyoyin mota  da dama a Jihar,  da  kyautatawa ma’aikatan Jihar ta hanyar biyansu albashi a duk wata. Kafin karshen wata ya kare, gwamna MA Abubakar yake biyan albashi a Jihar Bauchi. Don haka na dauki nauyin  kungiyoyi da dama a Jihar nan, don su shiga lungu da sako na Jihar nan, su  wayar da kan al’ummar jihar kan ayyukan alheri da gwamna M A Abubakar ya yi a jihar nan’’.

  Alhaji Abdullahi Zabala ya ce soyayyar da gwamnan  yake yiwa talakawan Jihar  ta hanyar kyautata rayuwarsu tare da rike amanarsu  ya sanya wasu suke adawa da shi a Jihar.

  Don haka ya yi  kira ga al’ummar Jihar Bauchi su fito kwansu da kwarkwatarsu su sake  zaben  gwamnan  a wannan zabe da za a gudanar, domin ya cigaba da wadannan ayyuka da ya sanya a gaba.

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here