Ana Zargin Akpabio Na Kokarin Maye Gurbin Abba Kyari

0
932
Daga Mustapha Imrana Abdullahi
WADANSU bayanai daga Jihar Akwa Ibom na cewa bisa dukkan alamu na cewa ana zargin tsohon shugaban marasa rinjaye Sanata Godswill Akpabio Na Kokarin Maye Gurbin shugaban ma’aikatan Gidan Gwamnatin fadar shugaban Nijeriya Abba Kyari.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta bayyana cewa a wadansu Awoyi Arba’in da Takwas da suka gabata Sanata Akpabio ya samu yin ganawar sirri tare da wani makusancin shugaban kasa da kuma wasu manyan jiga jigan Gwamnati ana zargin sun tattauna wannan batu.
Ana batun cewa shirye shiryen bashi wannan mukamin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, saboda ana tunanin yin hakan zai magance maganganun da ake yi cewa wadansu sun zagaye shugaban kasa da ake kira (Kabal) domin an samu wani mutum daga yankin kudu maso kudancin Nijeriya a bashi wannan muhimmin matsayi, wanda da hakan za’a magance duk wasu kalamai da wasu ke yadawa barkatai.
Ana ganin cewa idan an nada Akpabio a wannan matsayi al’amura za su daidaita kuma ana saran shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci Jihar Akwa Ibom a ranar Litinin domin yi wa Jama’a bangajiya tare da yin gagarumin taron daukacin jama’a daga bangarori daban daban.
Bayanan sun ci gaba da cewa wadansu daga cikin ma’aikatan fadar shugaban kasa tuni har sun isa babbar birnin Jihar Uyo inda suka sauka a Otal din Bexco da ke lamba 24 Abel Damina da ke rukunin gidaje na Osongama a birnin Uyo na Jihar Akwa Ibom.
Sai kuma wadansu ma’aikatan fadar shugaban kasar da za su kai ziyara Jihar Imo su wuce Dalta duk ana saran shugaban kasa zai Kai ziyara.
 Majiyar ta fadar shugaban kasa ta bayyana mana cewa daga cikin abin da Akpabio ke kokarin yi shi ne ganin ya yi amfani da taron da za a yi domin bukatarsa ta biya game da manyan jami’an hukumar zabe domin ganin Jam’iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben Jihar Mai arzikin man fetur.
TSOHON Gwamnan Akwa Ibom ya taba yin wani kokarin makamancin wannan zuwa fadar shugaban kasa lokacin tsohon shugaban Goodluck Jonathan a kokarinsa na jayayya da Ritimi Amaechi,wanda daga baya a fita daga PDP a wani yanayi Mai daure Kai.
An nada Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa a ranar 27 ga watan Agusta 2015.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here